✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kudin magada N385m suka yi batan dabo a Hukumar Shari’a ta Kano

Asiri ya fara tonuwa ne yayin da wani mutum ya yi kara kan wasu kudadensa.

A yanzu haka, wadansu magada a Jihar Kano sun shiga zullumi kan bacewar kudin gadonsu har Naira miliyan 387 a lalitar Hukumar Kula da Kotunan Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano.

Aminiya ta gano cewa an ajiye kudin magadan ne sakamakon jiran lokaci da ake yi don raba kudin ga magadan saboda rashin kammaluwar wasu abubuwa.

An ce asiri ya fara tonuwa ne yayin da wani mutum ya yi kara a kotu a kan wasu kudinsa Naira miliyan 40 da yake bin mahaifin magadan bashi sakamakon wata mu’amalar kudi da suka yi da shi kafin rasuwarsa.

Lokacin sauraron shari’ar, alkalin ya tabbatar da wannan mutumin abokin kasuwancin mahaifin magadan ne, inda kuma ya ba da umarnin a biya shi hakkinsa, sai dai kuma a daidai lokacin da aka nemi a fitar da kudin a Bankin Stanbic IBTC inda a can ne kudin suke ajiye sai aka tarar babu kudin sai ragowar Naira miliyan tara.

Binciken Aminiya ya gano cewa ana zargin wadansu ne suka rika kwaikwayon sa hannun wadanda suke da alhakin fitar da kudin daga asusun bankin inda kuma suka rika yi wa kudin dauki dai-dai.

Lokacin da Aminiya ta tuntubi Hukumar Kula da Kotunan Shari’ar Musulunci ta Jihar Kano ta tabbatar cewa an yi mata wannan wasosso kuma a cewarta ta tashi haikan wajen bincikar lamarin tare da daukar mataki a kan duk wanda yake da hannu a cikin harkallar kudin.

Sai dai a daidai lokacin da shugabannin Hukumar Kula da Kotunan Shari’ar Musulunci suke kokarin kafa kwamitin da zai binciki harkallar da aka yi da kudin magadan sai ga shi an nemi kwamfutocin ofishin guda bakwai an rasa.

Aminiya ta gano cewa sace kwamfutocin ba ya rasa nasaba da dakile binciken da ake shirin fara yi kasancewar duk wasu bayanai da suka shafi batun kudin an taskance su a cikin wadancan kwanfutoci.

Ustaz Haruna Khaleel shi ne Babban Magatakardan Kotunan Shari’ar Musulunci na Jihar Kano ya bayyana cewa duk wadanda suke da hannu a cikin wannan laamri ba za su kai labari ba domin asirinsu yana gab da tonuwa.

A cewarsa kuma sace kwamfutocin da aka yi a hukumar an yi a iska. “Daraktan Kudi ne ya zo yake shaida min cewa ba a ga wadanann kudi a asusunmu ba. Abin a aka iya samu shi ne Naira miliyan tara. aga nan muka je muka sanar a Alkalin Alkalai kan halin a ake ciki ina kuma muka kafa kwamitin on fara bincike,” inji shi.

Aminiya ta nemi sanin halin a binciken a Hukumar Karbar Korafe-korafe a Yaki a Almunahana ta Jihar Kano ina shugabanta na riko Barista Mahmu Balarabe ya ce bincikensu ya yi nisa a kan lamarin on kuwa sun fara gayyato masu ruwa-a-tsaki a cikin maganar.