✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kisan direba ya hassala direbobin tanka a Legas

A kwanakin baya ne wani direban motar tanka ya gamu da ajalinsa a hannun wasu jami’an hukumar kula da cinkosan ababen hawa na Jihar Legas,…

A kwanakin baya ne wani direban motar tanka ya gamu da ajalinsa a hannun wasu jami’an hukumar kula da cinkosan ababen hawa na Jihar Legas, wadanda aka fi sani da LASTMAN, lamarin da ya sanya direbobin manyan motocin rufe babban hanyar Oshodi zuwa mil 2 baya ga haka kuma direbobin sun rufe babbar hanyar nan ta mashigar Legas da ke Ogere har na tsawon sa’a 3, matakin da ya dakile hada-hada, duba da muhinmmacin hanyar; domin ita ce mashigar da ta hade Jihar Legas da sauran jihohin Najeriya.
Shugaban kungiyar direbobin motar tanki reshen garin Ogere Alhaji Baba Ibrahim Osajibo ya shaida wa Aminiya cewa yaran direban motar da ’yan LASTMAN din suka kashe ya shaida masu yadda lamarin ya afku.  Ya ce direban mai suna Salisu Sani dangwari ya faka motar ne a gefen hanya da sanyin safiyar Juma’a domin ya yi Sallah, ana cikin haka ne sai jami’an na LASTMAN suka cin masu, suka kama motar, ganin haka sai direban ya ga suna kokarin jan motar zuwa ofishinsu. Sai ya ce musu akwai kayansa a cikin motar su bari ya dauka. Da ya shiga gaban motar ta daya gefen sai daya daga cikin jami’an ya janyo shi kasa, daman dayansu ya hau motar. Koda ya tada ita sai ya take direban da abokin aikinsa ya janyo kasa. An yi kokarin kai direban asibiti amma sai rai yayi halinsa.Alhaji Baba Osajibo ya kara da cewa ba wannan ne karo na farko da ’yan LASTMAN suke kashe masu direbobi ba. “Ai daman babu wulakantacce a idon jami’an tsaron kasar nan da ya wuce direba, ’yan sanda su kashe, sojoji su kashe, haka su ma ’yan LASTMAN su kashe. Muddin kungiyoyin direbobi da na masu manyan motoci ba su dauki kwararan mataki ba sai an kai ga lokacin da za a ce wa direba zo ga lodin Legas ya ce ba za shi ba.” Inji shi, kana ya yi tir da rikon sakainar kashi da kungiyoyin masu manyan motoci suke yi da hakkokin direbibinsu.
“Wadannan kungiyoyin na samun sama da Naira miliyan dari a kowace rana amma wasu tsirarun mutane ne kadai ke cin gajiyar abin, babu wani abun a zo a gani da suke tsinanawa, in ban da kungiyar NURTW da take gina gidajen baki inda take sama wa daruruwan mutane ayyukan yi. Don haka ina kira ga Shugaba Buhari da ya juyo da kyawawan tsare-tsarensa a kan wadannan kungiyoyin; domin jama’ar kasar nan su fa’idantu da su. Ya kamata Gwannatin Tarayya ta duba hakkin direbobin nan duba da irin cin kashi da kisan kare dangin da jami’an tsaron kasar nan ke yi musu. Ai su ma direbobin mutane ne kamar kowa kuma ayyukansu na matukar ba da gudunmawa a ci gaban kasa.” Inji shi.
Sarkin Hausawan Ogere Alhaji Abdullahi Abubakar Saminaka ya shaida wa Aminiya cewa matakan da direbobin suka dauka na rufe hanyar bai dace ba, domin yin haka shi zai ba bata gari damar yin kone-kone, in kuma hakan ya afku su dai ’yan Arewa za su fi kowa cutuwa, domin a cikin dubannin manyan motocin da ake fakawa a garin Ogere, kashi 95 bisa dari na ’yan Arewa ne.
“To me za su ce in aka sanya wa motocin iyayen gidansu wuta? Don haka da ni da shugaban kungiyar direbobin motar tanka na nan Ogere muka yi makarbiya don kwantar da hankalin direbobin da suka hassala kuma da taimakon soji wadanda suka tarwatsa su, suka bude wa jama’ar hanya.” Inji Sarkin Hausawan Ogere.
Jami’ar hulda da jama’a ta rundunar ’yan sandan Jihar Legas Dolapo Opeyemi Badmus, ta tabbatar da faruwar lamarin. Ta ce tuni hukumar ta tura jami’anta wajen da lamarin ya abku domin kare abkuwar tarzoma.