✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kayan hada rabobi ka sa kankancewar al’aura —Bincike

Jinsin dan Adam na fuskantar barazanar haihuwa, inji Dokta Swan

Binciken masa kimiyya ya gano cewa shakar wani sanadari da ke gurbata muhalli na kawo kankancewar mazakuta.

Binciken ya gano cewa shakar iskar sinadirin phthalates, wanda ake hada kayan robobi da shi na kuma sa a haifi jarirai da tawaya a al’aurarsu.

Masaniyar Kimiyyar Muhalli, Dokta Shanna Swan, wadda ta jagoranci binciken, ta bayyana cewa mazakutar mutane na kankancewa, ana kuma samun masu tawaya mazakutarsu sakamakon gurbatacewar muhallin da sinadarin ke kawowa.

Binciken ya kuma gano jariran da ake haifa da kankancewar mazakuta na karara raya sakamakon yadda mutane ke kara shakar gurabtacciyar iska ta dalilin sinadarin.

Ya kuma gano cewa dan tayin da aka shaki sinadarin na phthalate a lokacin da ake dauke da cikinsa, na iya samun tawaya a al’aura ko kuma kankacewarta.

Kafar yada labarai ta SkyNews ta ta kasar Amurka ta ruwaito masaniyar na yin gargadin ne a sabon littafinta, wanda a cikinsa ta fayyace abubuwan da ke barazana ga lafiyar haihuwar dan Adam.

Littafin mai suna ‘Count Down’, ya yi zuzzurfan bincike ne kan “yadda yanayin rayuwar zamani ke kawo raguwar maniyyi da sauyi a lafiyar haihuwa tsakanin mata da maza da kuma illar hakan ga jinsin dan Adam a nan gaba”.

Ta bayyana cewa mutane na fuskantar “barazar raguwar” lafiyar haihuwa sakamakon shakar sinadarin phthalates, wanda ake amfani da shi wajen hada kayan robobi, wanda kuma ke da illa ga kwayar halittar dan Adam.

Ana amfani da sinadarin phthalate ne wajen sanya wa kayan robobi saukin sarrafawa domin yin kayan amfani, kamar kayan wasan yara.