Gwamnan Borno, Babagana Zulum, ya nuna damuwa matuka karuwar karuwanci da shaye-shaye a sansanonin ’yan gudun hijira na jihar.
Ya ce rashin tsaro da aikin yi na daga cikin abubuwan masu sa matasa shiga kungiyar ta’addanci, inda ya roki sojoji da su kwato gonaki don matasa su koma sana’ar noma.
Zulum ya bayyana hakan ne a lokaci ziyarar aiki da Kwamitin Majalisar Dattawa kan Ayyuka na musamman ya kai masa a Maiduguri.
Gwamnan ya bukaci kwamitin ya kalli karuwar yawan matasa da ake samu a kananan hukumomin Borno, wanda ya ce “Abun damuwa ne; da muka je Monguno kwanakin baya mun iske ’yan gudun hijira fiye da mutum 700,000.
“Karuwar lalata yara kanana da karuwanci da kuma shaye-shaye da ake yi a sansanin ’yan gudun hijira abun damuwa ne”, inji Zulum.
Ya roki kwamitin ya tausaya wa halin da ‘yan gudun hijira suke ciki su mayar da su garuruwansu ko wurare masu tsaro don su ci gaba da rayuwa.
Ya ce idan har ana son rage shigar matasa cikin kungiyar ta’addancin to sai an samar musu ayyukan yi.
“A yanzu matasa da dama na shiga kungiyar sakamakon rashin ayyukan yi”.
Ya ce idan har ba a kwato gonakai ba, matasa suka samu aikin yi ba, to Hukumar Habbaka yankin Arewa ta gabas (NEDC); da ta Bayar da Agaji Gaggawa (NEMA) za su gaji da kawo dauki a jihar.
Zulum ya ce gwamnatinsa ta gaji matan da suka rasa mazajensu 53,000 da marayu 54,000, kuma “yawansu na iya fin haka idan ba aka gudanar da kirgar ba a gwamnatance ba”.