✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda kananan yara suka tsere bayan kwana 60 da garkuwa da su

Yaran sun bayyana irin halin da suka tsinci kansu a hannun masu garkuwar.

Wasu kananan yara ’yan gida daya da ba su wuce shekara 10 ba sun kubuto daga hannun masu garkuwa bayan kwashe kwana 60 a can.

Wadannan kananan yara sun shaida wa Aminiya cewa su 16 ne suka tsere daga hannun masu garkuwar, ciki har da wata mai jego da wata amarya daga da ’yan tawagarta da aka yi garkuwa da su gaba dayansu a hanyarsu ta kai amaryar dakin mijinta.

An yi awon gaba da yaran ne a ranar 9 ga watan Yuni, 2021 daga unguwar Dutsen Abba a Karamar hukumar Zariya, Jihar Kaduna, ba su suka shaki iskar ’yanci ba sai Allah Ya yi musu gyadar dogo a ranar Lahadi 8 ga Agusta, 2021.

– Halin da suka shiga daji

A zantawar da muka yi da su, sun bayyana irin halin da suka tsinci kansu a dajin a da ’yan bindigar suka ajiye su.

“Abinci sau daya ake ba su kuma shinkafa ne babu mai ko yaji a ciki, ga shi ba ma wanka, kuma sun hana mu yin sallah.

“Tun da muka je kayan da ke jikinmu shi ne a jikinmu har ranar da Allah Ya sa muka kubuto, sai dai ana kai mu rafi don mu yi wanka.”

A cewarsu, “Sai dai mu ba a daure mu ba kuma muna haduwa da sauran yaransu da yaran da aka yi garkuwa da mu muna wasanni tare.

“Da farko mun jarraba gudu muka bace muka kara kutsawa cikin daji maimakon hanyar shigowa gari, to sai muka kara komawa wajen da aka yi garkuwan da mu har sai wannan lokacin ne Allah Ya kaddara gudowammu.

“Kuma dajin da aka kai mu duk Fulani ne suna da shanu da yaransu ke kiwo, kuma akwai kusan daba ya kai uku kowacce da shugabanta; Sai dai namu daban akwai Hausawa guda biyu daga cikin shugabanninsu.”

Da yake nuna godiyarsa ga Allah, mahaifin yaran, ya kara da cewa, “A ranar Lahadi 8 ga watan takwas sai aka bugo mana waya daga gidan Dakacin Sabon Birini, cewa ga wasu yara uku daga cikin wadanda Allah Ya sa suka kubuto, sai nan da nan muka nufi garin don dawowa da su.

“Da ma yaran nawa suna cikin mutum 11 da aka sace a garin namu, amma an sako wasu daga ciki bayan biyan kudi har miliyan uku da kuma babur daya.

“Sai suka kara rike su yaran nawa cewa wai sai an kara musu kudi sai kuma ga shi rokon Allah Ya sa sun kubuto daga hannunsu.”

Ya bayyana cewa daga cikin yaran da suka kubuto akwai mace mai shekara 10 da kannenta biyu — mace mai bakwai da watanni, da kuma kaninsu mai shekara bakwai.

Yaran, bayan an kai su asibiti domin duba lafiyarsu, yanzu haka sun koma gida suna tare da sauran ’yan uwansu.

Hoton Dakacin Dutsen Abba Alhaji Nuhu Abdullahi Falalu