✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda jam’iyyu suka kacaccala kujerun sanatoci a Zaben 2023

Akalla jam’iyyu takwas ne za su samu wakilci a Majalisar Dokokin Tarayyar ta 10.

Jam’iyyar APC mai mulki ta ci gaba da kasancewa mai mafi rinjayen kujeru a Majalisar Dattawa, inda ta samu karin kujeru hudu bayan kammala zaben da aka yi a ranar Asabar da ta gabata.

A karshen makon da ya gabata ne Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta gudanar da zabubbukan wasu ’yan Majalisar Dattawa guda bakwai da suka hada da jihohin Yobe, Kebbi, Sakkwato, Zamfara da Filato.

An dai gudanar da zabukan cike-gibin ne wadanda tun farko INEC ta ayyana cewa ba su kammala ba sakamakon wasu dalilai da ciki har da aringizon kuri’u da tashi-tashina yayin gudanar da zaben a karon farko.

Gabanin zaben na karshen makon jiya, jam’iyyar APC mai mulki ta samu kujeru 55 tun a zaben ’yan Majalisar Dokokin Tarayyar da aka gudanar a ranar 25 ga watan Fabrairu.

Sai dai kuma bayan zaben bayan nan, a yanzu tana da adadin sanatoci 59 da aka zaba a karkashin inuwar jam’iyyar ta APC.

Akalla jam’iyyu takwas ne za su samu wakilci a Majalisar Dokokin Tarayyar ta 10, lamarin da ya sa za ta kasance daya daga cikin mafi hadin-gambiza a tarihin Najeriya.

A halin yanzu jam’iyyar PDP tana da Sanatoci 36, jam’iyyar Labour (LP) tana da takwas, yayin da jam’iyyar NNPP da SDP kowannensu ke da kujeru biyu.