✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda jami’in tsaro ya haddasa tsoro a Gombe

Ya markade yara 8 da mota ya raunata 35   Aranar Lahadin da ta gabata da dare ne wani jami’in tsaro na Hukumar Kula da…

  • Ya markade yara 8 da mota ya raunata 35

 

Aranar Lahadin da ta gabata da dare ne wani jami’in tsaro na Hukumar Kula da Tsaro ta Fararen Hula (NSCDC) mai suna Adamu Abubakar wanda aka fi sani da Ukasha ya jefa tsoro a zukatan jama’ar birnin Gombe, bayan da ya hallaka yara 8 tare da raunata 35 a daidai lokacin da suke gudanar da bukukuwan Ista don tunawa da mutuwa da tashin Yesu Almasihu a garin Gombe fadar Jihar.

Al’ummar jihar sun shiga jimami kan yadda wannan jami’i ya tuka mota ya take yaran wadanda mambobin Kungiyar Boys Brigade ne da mortarsa a daidai lokacin da suke tattakin bikin Ista.

ASC Abubakar da abokinsa mai suna Murtala Hassan da ake yi wa inkiya da Kwastam dan Unguwar Tudun Wadan Gombe nan take masu jerin gwanon da suka fusata suka kashe su.

Binciken da Aminiya ta yi ya gano cewa Ukasha jami’i ne na Sibil Difens da aka tura shi aiki a gidan gwamnati a matsayin jami’in hukumar da ke tsakaninsu da gwamnati wato Liaison officer. Kuma wata majiya da ke gidan gwamnati da ta nemi a sakaye sunanta ta tabbatar wa wakilinmu cewa Ukasha yana gidan gwamnati fiye da shekara goma.

“Kafin tura Ukasha gidan gwamnati ya taba zama dogarin tsofaffin Kwamishinonin Ilimi biyu na jihar Dokta Habu Dahiru da kuma Malam Labilwa Ahmadu Madugu,” inji majiyar.

Majiyarmu ta ce an samu takaddama a tsakanin Ukasha da yaran ne wadanda suka fito daga Cocin Ecwa na Unguwar Bamusa da Barunde da Cocin Angilika na St Peter’s da ke Unguwar Madaki a Gombe suke tattakin ista da misalin karfe 11:30 na dare a ranar Lahadin lokacin da suka nufi Titin Unguwar Sabon Layi don bikin Ista da za yi a washegari Litinin.

Wata majiya ta ce, bayan an samu takaddama a tsakanin Ukasha da yaran, sai ya wuce a motarsa ta aiki kuma daga baya, sai ya juyo ya kashe wutar motar ya auka wa yaran ya kashe 8 daga cikinsu nan take tare da raunata 35. Nan ne mambobin Kungiyar Boys Brigade da suka tsira suka bi shi a guje suka hallaka shi tare da abokin tafiyarsa, inda adadin wadanda suka rasu ya koma 10.

Wadansu da suka san Ukasha sun shaida wa Aminiya cewa mutum ne mai zafin rai da bai barin ko-ta-kwana wanda idan aka yi masa abu sai ya rama kuma ba ya da yafiya.

Da farko an rika yada jita-jitar cewa abokin nasa dan sanda ne amma wata sanarwa da hedkwatar ’yan sandan jihar ta fitar a ranar Talata ta ce Murtala Hassan ba dan sanda ba ne ma’aikacin gwamnati ne. Murtala Kwastam, ma’aikaci ne a ofishin Babban Mai Binciken Kudi na Kananan Hukumomin Jihar Gombe.

Lokacin da wakilinmu ya ziyarci gidan iyayen Murtala Hassan a Unguwar Tudun Wada ya tarar da dimbin mutane suna zuwa ta’aziyya amma babu wanda ya yarda ya zanta da ’yan jarida a kan lamarin.

Wakilinmu ya ziyarci Unguwar Railway inda aka samu yara biyu suke cikin wadanda aka kashe da kuma wanda ya tsira da rauni mai suna Joel Nanyak wanda ya shaida masa cewa da misalin karfe 11:30 na dare a kan hanyar Gombe zuwa Biu, suna kade-kadensu sai wannan mai motar ya zo wucewa aka hana shi bi ta cikinsu har ta kai an yi ja-in-ja daga bisani aka bar shi ya wuce. “Bayan ya wuce ne sai ya ce ai zai dawo za su ga abin da zai yi,” inji Joel Nanyak.

Ya ce “A lokacin su biyu ne da ’yan mata biyu a motar, can bayan ya ajiye su sai suka dawo ba ’yan matan sai ya kunna fitilar motarsa ya kashe har sau uku can sai ya kashe fitilar kawai ya yi kanmu ya rika taka mu inda na take ya kashe yara 8 wadansu da yawa suka ji rauni. Shi ma aka kashe shi shi da wanda suke motar tare.”

Ya ce “Bayan ya tattaka mutane ne sai na ga har da kanena mai suna Joseph dan shekara 18, ni ma kuma na ji rauni a kafa amma da sauki.”

Mista Danjuma Paul, tsohon Ma’aikacin Hukumar Jiragen Kasa ta da ya rasa dansa Joseph Danjuma da ke aji uku a karamar sakandare ta Unibersal Nursery and Primary School ya bayyana jimaminsa kan rashin dan nasa.

Mista Danjuma, ya ce duk shekara suna bikin tunawa da mutuwa da tashin Isa Almasihu a matsayinsu na mabiya addinin Kirista kuma ’ya’yansu suna fita cikin jerin gwano don alamta bikin ranar tashin nasa. Shi ne a wannan lokaci bayan sun fita sai suka samu mummunan labari a kan ’ya’yansu na kashe su da aka yi.

Magidanci da yake da ’ya’ya hudu ya ce lokacin da yaran nasa suka fita jerin gwanon daya daga cikinsu mace ta dawo gida uku, can sai daya ya dawo gida ya rika buga musu kofa cewa a bude masa, mota ta kashe yayansu. “Shi ne na tashi na fita na je na ga gawarsa da sauran da aka kashe sai na dauki dangana a kan Allah ne Ya kawo hakan, dole kuma mu yi hakuri aka tafi da su dakin ajiye gawarwaki na Asibitin Kwararru na dawo gida,” inji shi.

Mista Danjuma, ya ce maganarsa ta karshe da dansa Joseph da mahaifiyarsa ita ce da zai fita sun yi masa fatan a je lafiya a dawo lafiya ban da fada ban da tashin hankali, shi ne bayan ya fita sai suka ji mummunan labari a kansu.

“Joseph shi ne mai buga babbar gangar ’yan Boys Brigade kuma shi ne babban dana, amma tunda Allah Ya dauki kayanSa dole mu dauki hakuri,” inji shi.

Ya ce da ya ji cewa wanda ya aikata wannan danye aiki jami’in hukuma ne na Sibil Difens wanda ya kamata ya kare rayukan al’umma da dukiyoyinsu sai ga shi ya aikata haka sai ya ce yana bai wa gwamnati shawara ta fara tantance lafiyar kwakwalwar jami’an tsaro wajen yi musu gwaji gudun kada su rika kashe mutane haka kawai.

Mista Danjuma, ya ce ya samu labarin cewa jami’in Adamu Abubakar Ukasha bai jima da fitowa daga gidan kurkuku ba bisa zarginsa da kashe yarinyarsa da ya yi aka daure shi.

Shi ma Mista Amos Ibrahim mahaifin marigayi Irimiya Amos, da ya rasu a jerin gwanon ya bayyana kaduwarsa kan yadda Irimiya mai shekara 14 ya gamu da ajalinsa ta wannan hanya.

Mista Amos, ya ce Irimiya, shi ne dan autansa kuma yana aji uku na karamar sakandare ta ’ya’yan sojoji (Army Children School) da ke Barkin Soja na Gombe.

“Na yi rashin abokin shawara,” inji mahaifin wand ya ce maganarsu ta karshe da Irimiya ita ce da zai tafi faretin ya ce a saya masa batirin wayarsa don ya karbo ta a wajen gyara. Sai na ce masa a dawo lafiya kalmata ta karshe da shi ke nan. Na dauki kaddara tunda wannan lamarin daga Allah ne fatanmu shi ne Allah Ya yi mana ta’aziyya,” inji Mista Amos.

A cewarsa har zuwa lokacin rubuta labarin gwamnati ba ta yi musu ta’aziyya ba, Kungiyar Kiristoci (CAN) da Cocin ECWA ne kadai suka aike musu da ta’aziyya.”Mun rungumi kaddara fatanmu kawai shi ne ’ya’yanmu su samu biso mai kyau,” inji shi.

Elder Yusuf Samanja, mahaifin Polina Yusuf, ya ce lokacin da lamarin ya faru da ’yarsa ya je kauye ta’aziyyar rasuwar

 

Bappansa kwatsam sai ya ji labari mai ta da hankali na rasuwar Polina.

Polina tana aji shida a makarantar firamare ta Bogo, inji Babanta wanda ya ce kafin ya tafi kauyen ta sce masa idan ta gama firamare Kwalejin ’Yan Mata ta Doma take son zuwa saboda makarantar kwana ce idan tana can za ta yi karatu sosai.

Elder Yusuf Samanja, ya ce ita ce ’yarsa ta hudu kuma yana jin dadin yadda yake ganin al’amuranta. A cewarsa maganarsa ta karshe da ita shi ne a lokacin da zai tafi kauye ta’aziyyar ta ce masa idan ya je ya gaisar mata da sauran ’yan uwanta na kauye kawunanta ya ce mata zai ce musu tana gai she su idan ya je.

Y a ce yana son gwamnati ta dauki mataki a kai amma shugabannin Kungiyar Boys Brigade su suka fi sanin matakin da ya kamata a dauka tunda a gabansu komai ya faru idan ma kuskure ne ko ganganci.

Shi ma Mista Samson, mahaifin Miracles Samson wadda ta karye a wuri biyu da Ruth Samson wadda ta rasu, cikin kuka da tashin hankali ya ce ba zai ce komai a kai ba domin sun yi taro da shugabanin Kungiyar Kiristoci CAN a kan lamarin.

Ya ce Ruth ta rasu ga Miracles a gida an ki kula da su a asibiti kuma ga karaya waje biyu hankaliinsa ba a kwance yake ba wadansu ’yan jarida ma sun zo don yi masa tambayayoyi ya ce bai da abin fada fatarsa Allah Ya ceto masa ran Miracle kada ta rasu ko zai samu saukin tashin hankalin.

Ya ce batun yi wa ’ya’yansu biso mai kyau tuni Mukaddashin Sakataren Gwamnatin Jihar, James Pisahgi, ya yi magana da gwamnati don haka ba matsala.

Ganin wanda ya haddasa hatsaniyar jami’in Hukumar Cibil Defence mai mukamin mataimakin sufurtanda, Aminiya ta nemi jin ta bakin Kwamandar Hukumar ta Jihar Gombe Hajjya Altine Sani Umar, amma lokacin da ta je hedkwatar ba ta samu ganinta ba, amma wata majiya ta shaida mata cewa lailai jami’insu ne amma ba su suka tura shi ba domin lokacin da abin ya fara cikin dare ne ba lokacin aiki ba.

Da wakilinmu ya tuntubi Shugaban Kungiyar Boys Brigade, Adams Borkono, ta waya don jin ta bakinsa ya ce ba ya gari ba zai iya cewa komai ba sai ya shigo gari kuma ba zai yi magana ta waya ba saboda wadansu ’yan jarida sun buga labarin ba tare da sun tuntube shi ba.

Kakakin Rundunar ’Yan sandan jihar Gombe, SP Mary Obed Malum, ta tabbatar da faruwar lamarin inda ta ce mutum 10 ne aka tabbatar da rasuwarsu a hadarin.

Malum, ta ce 8 daga cikin 10 mambobin Kungiyar Boys Brigade ne sauran 2 kuma direban motar da ta kashe su ne da abokinsa da suke tare.

Sannan ta ce yanzu haka ’yan sanda sun dukufa bincike don gano masabbabin wannan hadari.

Kyaftain din Boys Brigade na Cocin Ecwa Bogo Michael Achika, ya roki gwamnatin Jihar Gombe ta biya kudin magungunan waddnda suka ji raunuka.

Achika ya kuma roki gwamnati ta biya diyya ga iyalan wadanda suka rasa rayukansu.

Ya jinjina wa ma’aiakatan lafiya na Asibitin Kwararrun kan yadda cikin gaggawa suka kula da wadanda aka kawo musu.

A bangaren Malaman Addinin Musulunci Mataimakin Shugaban Majalisar Malamai ta Kasa ta Kungiyar Jama’atu Izalatil Bidi’ah Wa Ikamatis Sunnah Sheikh Usman Isa Taliyawa, ya bayyana cewa wannan lamari ne marar dadi, musamman ganin ana zaune lafiya a tsakanin Musulmi da Kirista a Jihar, inda ya ce irin wannan abu yana iya kawo tashin hankali. Ya mika ta’aziyya ga iyayen yaran

Cikin yara 35 da suka jikkata wadansu sun yi karaya bibbiyu, wadansu daya wadansu gurdewar inda 13 suke jinya a Asibitin Kwararru na Jihar, sai 13 a Asibitin Sabana, biyu sa Asibitin Saleem, hudu a Asibitin Koyarwa na Tarayya da Asibitin Doma sannan biyu kuma suna jinya a gida.

Yara 8 da suka rasu kuwa su ne Jessy John da Irimiya Amos da Joseph Paul da Sunday Samuel da Ruth Samson da Paulina Yusuf da Keziah Amos da kuma Joseph Daniel.