✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda jami’an tsaro suka kashe mai jego da jaririyarta

’Yan sanda sun tabbatar cewa jami'an tsaron Sibil Difens sun harbe wata mai jego da jaririyarta ’yar wata takwas har lahira a Jihar Imo

’Yan sanda sun tabbatar cewa jami’an tsaron Sibil Difens sun harbe wata mai jego da jaririyarta ’yar wata takwas har lahira a Jihar Imo.

Rundunar ’yan sandan jihar ta bayyance cewa harsashin da jami’an suka harba ya yi ajalin mai jegon da jaririyarta ne a bisa kuskure, amma ba su ya harba ba.

Wasu majiyoyi a jihar sun ce harsashi ya samu wata mata kuma da ake tunanin mahaifiyar mai jegon ce.

Kakakin rundanar ya ce jami’an NSCDC sun yi harbi ne a iska daga kan motar sintirinsu da ke tafiya, amma aka yi rashin sa’a harsashi ya samu jaririmatar da ’yarta a lokacin da take jiran motar haya.

Aminya ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne a ranar Lititin a Mahadar Fire Service da ke garin Owerri, babban birnin jihar.

Okoye ya ce, “Ana gudanar da bincike, amma wani ganau ya shaida mana cewa harsashin jami’an Sibil Difiens ne ya samu matar da jaririyarta; da aka kai su asibiti kuma likita ya tabbatar cewa sun rasu.”

Amma ya ce duk da bayanin ganau din, za aci gaba da bincike.