✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Yadda jama’ar gari suka kama dan bindiga da hannu a Katsina

Dubunsa ta cika a lokacin da ya je sayen miyagun kwayoyi a Jibiya.

Wani da ake zargin dan bindiga ne ya gamu da ajalinsa bayan mutanen  gari sun yi masa kofar rago sun kama shi da hannu a Jihar Katsina.

Mutanen garin Magama da ke Karamar Hukumar Jibiya ta Jihar Katsina sun yi wa shi wannan dan bindiga mai suna Baleri dirar mikiya ne bayan ya yi shigar burtu a hanyarsa ta zuwa sayen miyagun kwayoyi a garin.

Kan ka ce kwabo mutanen suka rika jibgar sa, sai daga baya ’yan banga suka kwace shi suka mika shi ga sojojin da ke sintiri a garin.

Daga bisani kuma aka tsinci gawar dan bindigar a kusa da kauyen Kukar Babangida da ke Karamar Hukumar ta Jibiya.

Har zuwa lokacin da muka kammala hada wannan rahoto babu wani cikakken bayani game da yadda dan bindigar ya mutu.

Bayan an tsinci gawar tasa, wasu mutum uku daga cikin ’yan uwansa sun zo za su dauki gawar, amma jami’an tsaro suka tsare su.

Karamar Hukumar Jibiya na daga cikin sassan Jihar Katsina da hare-haren ’yan bindiga suka hana sakat, musamman a baya-bayan nan.

A baya-bayan nan gwamnatin Jihar ta rufe layukan sadaruwa a kananan hukumomi hudu, ciki har da Jibiya a yunkurinta na karya lagon ayyukan masu garkuwa da mutane a yankunan da matsalar ’yan bindigar ta fi kamari.