Kungiyar yaki da rashawa da binciken bayanai ta (ARDI) ta bukaci hukumar yaki da cin hanci da rashawa (ICPC) ta binciki hukumomin gwamnatin da ake zargi da yin kazamar rashawa.
Kungiyar ta yi zargin rashawa a hukumar habbaka yankin Neja Delta (NDDC) da hukumar kula da yanayi (NIMET) da hukumar habbaka yankin Arewa maso Gabas (NEDC) da hukumar inshowa ta NSITF da sauransu.
Daraktan watsa labarai na ARDI, Yiniyes Jibrailu a wata wasikar da ya rubuta wa ICPC ya bukace ta da ta yi bincike kan dukiyoyin ‘yan Najeriya da aka sace tare da bayyana sakamakon binciken da matakan da aka dauka.
Kungiyar da ta bankado korafin da ya yi sanadiyar tsohon Ministan Shari’a, Walter Onnoghen ya rasa kujerarsa, ta tunatar da ICPC cewar bincike kan rashawa da sanar da ‘yan kasa matakin da aka dauka na daga cikin dalilan kafa ta.
Ya ce sanin kowa ne ma’aikatan gwamnati na gina gidaje na alfarma da hawa manyan motoci, su kuma kai ‘yayansu makarantu masu tsada a kasashen waje, amma babu mai bincikar inda suka samu dukiyar.
Wasikar ta ce bibiyar lamurra da ARDI ke yi ya gano yadda ma’aikata ke yin yadda suka ga dama a ofisoshinsu da rashin bin ka’idojin kwangiloli.
Ya ce kamata ya yi ICPC jagoranci yakar matsalar amma bisa dukkan alamu ta sarayar da aikin ga kungiyoyin kare hakkin bil’Adama da kuma ‘yan jarida da ke watsa labaran almudahana.
Ya kuma nuna rashin gamsuwa da yadda ICPC ta bar binciken a hannun Majalisar Tarayya, ya ce hakan ya siyasantar da lamarin tare da mayar shi wasan kwaikwayo.