Yau ma za mu ci gaban nazarin da muka faro kan yadda Hausawa suke sarrafa harshe, inda muka kalato muku makalolin masana adabi daga bangarori daban-daban domin amfanin masu karatu da kuma daliban ilimi:
Ma’anar Zaurance
“Zaurance zance ne, mai hankali yake gane shi,” inji wani mawaƙin Hausa. Shi zaurance salo ne na magana da akan yi shi don a yi ɓad-da-bamin zance, ga wanda ba a son ya gane inda aka dosa. Muna iya kallonsa kamar wani yare ne na ɗan taƙaitaccen lokaci ake ƙirƙira a cikin Hausa, saboda gwanancewa a kan harshen Hausar. Masana harshen Hausa irin su Farfesa Ɗangambo (1984), da kuma Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yar’aduwa (1992), sun tabattar da zamowar zaurance ƙirƙirarren harshe.
Abin da ya sa aka kira shi da ƙirƙirarren harshe shi ne cewa wata ƙungiya ta wadansu mutane waɗanda suna ma iya zama mutum biyu ko fiye, waɗanda kansu ya haɗu sosai kan tsaya su tsara salon da za su riƙa yin maganar da ba mai iya gane ta sai su kaɗai a duk wurin da suka samu kansu.
’Yan mata su suka fi amfani da wannan salo na magana, musamman a wuraren da su ke son yin wata magana ta sirri wacce ba su son kowa ya ji sai su kaɗai.
Babban darasin da wannan salo na magana ke koyarwa shi ne riƙe sirri, neman shawarar juna, haɗin kai, amince wa juna, riƙon amana, da kuma son juna.
Ana yin zaurance ne ta hanyar ƙara wasu harrufa a ƙarshen kowace gaɓa da ke cikin kalma har zuwa ƙarshen zancen. Haka kuma babu wata ƙa’ida da aka ajiye cewa lallai sai harafi kaza za a yi amfani da shi. A’a, su masu yin su sukan zaɓi nasu salon, saboda haka ne ma za a ga cewa waɗannan ba su gane na waɗancan.
Misalin Zaurance
Jirkitacciyar magana: La ke ra ke bi ke yo ke, ta ke shi ke mu ke bar ke gu ke rin ke nan ke.
Ma’anarta: Larabiyo, tashi mu bar wurin nan.
Jirkitacciyar magana: Je ke ki ke za ke na ke bi ke yo ke ki ke, kar ke su ke ga ke ne ke.
Ma’ana: Je ki zan biyo ki, kada su gane.
Take
Take kiɗa ne ko busa da makaɗa kan kaɗa ko su busa wa wani mutum; yawanci masu sarauta ko sarautar kanta ko kuma wani jarumi, ko wani gari da sauransu. Haka ma samari da ’yan mata akan kaɗa musu take musamman a lokutan rawar kalangu. Makaɗan maza da makaɗan fada da makaɗan sarauta da makaɗan jama’a, su suka fi yin take.
Ma’anar Take
Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yar’aduwa (1992), sun siffanta take da cewa, “Take ɗan guntun amo ne da ake kaɗawa ko busawa da kowane irin abin kiɗa ko busa ba tare da waƙa ba. Amma masu kaɗa taken da waɗanda ake kaɗawa sun san abin da ake nufi da inda aka dosa da shi.”
Take yana keɓanta ne da wanda aka yi taken dominsa shi kaɗai! Wanda ka iya zama mutum ɗaya, ƙungiya, ko kuma wani gari da sauransu. Matuƙar aka ƙirƙiri take, aka kaɗa wa wani shi, to, ba dama kuma a yi amfani da wannan taken ga wani mutum daban ba shi ba.
Ana yin take ne da abin kiɗa ko busa, sannan a bi shi da magana domin mai sauraro ya fahimci abin da ake nufi da inda aka dosa. A wasu lokuta shi kansa kiɗan ko busar magana ce wadda sai mai yi da wanda ake yi wa suka fi ganewa. Amma akan samu wani maroƙi a irin wannan hali ya riƙa faɗin abin da ake kaɗawa ko busawa in har kiɗan ko busar na magana ne. A yanayin kiɗa akan samu makaɗin yana kaɗawa sannan kuma yana faɗin abin da yake kaɗawa, amma busa ba wannan damar dole a samu mai yin magana daban, kodayake shi ma kiɗa wasu lokutan akan samu mai kiɗa daban, haka nan mai faɗin maganar daban. Akwai kuma taken da zallar kiɗa ne ko busa; abin nufi, kiɗa ne kawai ko busa ba wata magana ake faɗi a cikin kiɗan ko busar ba.
Akwai dangataka tsakanin take da kirari a wasu lokutan. Kasancewar take kiɗa ne, to idan aka kaɗa wa mai shi, musamman jarumai kamar masu dambe, kokawa, farauta da sauransu, sukan taso suna kirari. Wannan gaɓar ita ta haɗa take da kirari. Amma kowane daga cikinsu gashin kansa yake ci. Shi take kiɗa ne, shi kuwa kirari magana ce.
Take wani abu ne mai matuƙar muhimmanci a Ƙasar Hausa. Saboda muhimmancinsa har ana gadonsa. Sai dai idan take na gado ne za a ji a cikinsa ana cewa, An sare ƙaya, ƙaya ta tofo, ko kuma Kyawun gida da magaji, ko kuma Kyawun ɗan ƙwarai ya gaji uba nai da sauransu. A cikin take akwai fa’idojin da suka haɗa da zaburantarwa, ƙarfafar gwiwa, taskace tarihi da al’adu, sarrafa harshe, fasaha da sauransu.
Habaici
Habaici salon magana ne da Bahaushe ke amfani da shi wajen isar da wani saƙo a hikimance ta cikin zance. Wannan saƙon zai iya kasancewa gargaɗi, huce haushi, jan-kunne da sauransu. Magana ce da ake yinta a cikin duhu; ma’ana, ba kai-tsaye ake fito da maganar ba, sai dai shi wanda ake yi dominsa ya san inda aka dosa. Ko kuma idan abin ya shafi wani laifi ne da mutumin ya aikata, to duk wanda ya san ya aikata laifin shi ma zai iya sanin inda aka dosa. Amma in ba haka ba, sanin inda aka dosa cikin habaici yana da wahala.
Ma’anar Habaici
Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yar’aduwa (1992), suka ce, “Habaici kalmomi ne da ake amfani da su a fakaice don muzanta mutum.”
Dalilan da suke sa yin habaici suna da yawa, daga ciki akwai tsokanar faɗa, jan-kunne, gargaɗi, ramuwa, kishi, ƙyashi, hassada, rowa, aikata wani abin ƙi da sauransu. Kowane ɗaya daga cikin waɗannan dalilai da aka zayyana da ma wasunsu, in suka faru sai a yi amfani da habaici a cusa wa wanda ake magana da shi haushi. Shi kuma Farfesa Ɗangambo (1984) cewa ya yi, “Habaici, wata hanya ce ta zagin mutum a fakaice.”
Hanyoyin da ake bi wajen yin habaici akwai gugar zana, karin magana, harbin iska da sauransu. Misali:
Idan wani ya shiga sabgar wani a wani lokaci, yana iya bari sai daga baya ya ce, “Daga yau in mutum ya ƙara shiga sabgata, sai na turmumusa hancinsa a ƙasa.” Ka ga wannan jan-kunne ake yi amma ta cikin habaici. Maimakon a ce wane daga yau in ka ƙara shiga sabgata zan yi maka kaza. Ko kuma a ce, wane, daga yau hawainiyarka ta kiyayi rama ta. A nan kuma an yi habaici ne mai kama da karin magana.
Idan wani ya sayi wani abu kamar abin hawa haka, ana iya bayyana hassadar da ake yi masa ta cikin habaici. Misali, a ce, “Mu ma dai mun kusa sayen motar nan.” Za a gane cewa hassada ce idan aka lura da cewa a nan mai faɗin maganar maimaikon ya taya wanda ya sayi motar murna sai ya ɓuge da cewa shi ma dai zai saya.
Idan wani ya nuna son ya mallaki wani abu, za a iya cewa da shi, “Nan gani, nan bari.” Ko kuma a ce “Kwalele dokin Iliya, ba ni sayar da kai, ba ni ba da aronka,” da sauransu.
Akwai dangantaka tsakanin habaici da zambo, saboda zamowarsu duk zagi ne da ake yi wa mutum ba tare da kama suna ba. Sai dai shi zambo yakan fito da siffar wanda ake zagi ta yadda kowa zai iya gane shi.
Zambo
Zambo, salon magana ne da ake amfani da shi wajen baƙanta wa mutum ta cikin hikima, ta hanyar bayyana siffofinsa sannan a danganta shi da aikin da ya aikata na muni. Wato a cikin zambo ana fito da surar mutum ne a fili, sannan a munana shi ta hanyar bayyanar da ɓoyayyen mummunan aikin da ya aikata. Akan siffanta mutum matuƙa ta yadda duk wanda ya san shi, da ya ji zai gane wanda aka nufa da wannan magana.
Ma’anar Zambo
Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yar’aduwa (1992), sun ce zambo, “Kalmomi ne na ɓatawa da ake amfani da su don a musguna wa wani. Akan kwatanta kama ko hali ko ɗabi’a da wasu munanan siffofi ko halaye don a wulaƙanta mutum.”
Zambo zagi ne. Farfesa Ɗangambo (1984), ya ce “zambo zagi ne na kai-tsaye, idan an kwatanta shi da habaici.” Yahaya, Zariya, Gusau da ’Yar’aduwa (1992), sun bayyana cewa wadansu sun ɗauki zambo zagi ne kuma kishiyar yabo.
Ke nan za mu fahimci cewa akwai dangantaka tsakanin zambo da habaici. Idan muka so ma muna iya cewa, wa da ƙane suke, bisa dogaro da jawabin Farfesa Ɗangambo (1984) da ya zo a sama. Wato a bayyane, da zambo da habaici duka zagi ne a ra’ayin Farfesa. Sai dai shi habaici ana sakayawa, ba kowa zai gane wanda ake zagi ba. Amma a cikin zambo, duk wanda ya san wanda ake zagi, to da ya saurari wannan zambon zai gane shi. Saboda haka shi zambo, wan habaici ne.
Ana yin zambo saboda dalilai masu yawa, daga ciki akwai:
Ƙiyayya tsakanin mutane kan jawo a yi zambo don a rage wa wanda ake ƙi daraja a cikin mutane, ko a jawo jama’a su ƙi shi. Wannan kuma a kan fake da wani aibi da mutum ya aikata komai ƙanƙantarsa, sai a kambama shi, a kururuta shi yadda abin zai yi muni sosai. Dubi waƙar Mamman Shata ta Gagarabadau. In da yake cewa “…shadidi, mazinaci…”.
Son fifita wani sama da wani. Kamar abin da ya shafi sarakuna, mawaƙansu kan yi zambo su ɓata ’yan uwansu don dai su mawaƙan su samu ɗaukaka a wurin sarakunan, sannan su jawo wa shi ɗayan baƙin jini a cikin jama’a. Dubi waƙar Sani Aliyu Ɗandawo ta Turaki Aminu Wan Maza, wurin da yake cewa: “’Yan Sarki sun raina mutane, ’yan Sarki sun raina mawaƙa, sun maishe mu ba mu san komai ba, in za su ba mu kyautar doki, wai su ramamme suka ba mu, ko wanda bai gani…”
Sannan ana yin zambo da nufin gargaɗi ko jan-kunne, ko ankararwa da sauransu.
Haƙiƙa akwai gwanintar harshe a cikin zambo, saboda duka ne ba kama suna. Ana amfani da wannan gwaninta ta harshe a yi raga-raga da mutuncin mutum, kuma ba dama ya fito ya yi magana, saboda ba a kama suna ba. Don haka da zarar ya amsa, to ya bayyana kansa ke nan. Caɓɗijam! Wani aikin sai Hausa.
Mun ciro wani sashi na rubutun daga littafin Junaidu I. da ’Yar’aduwa T.M. (2003) mai suna Harshe da Adabin Hausa a Dunƙule. Gudunmawar Farfesa Dangambo kuma daga Rumbun Ilimi na shafin Intanet.
Za mu ci gaba a makon gobe