Al’ummar garin Tudun Biri da ke Karamar Hukumar Igabi a Jihar Kaduna suna cike da mamakin yadda garinsu ya yi fice a cikin kwana 34, lamarin da ba su tsammaci hakan ba a rayuwarsu idan suka dubi inda kauyen yake.
Ficen da garin ya yi a Nijeriya da duniya ya fara sauya garin ta hanyar kawo abubuwan ci gaba tare da sauya rayuwar mutanen garin, kuma hakan ya biyo bayan harin bam din da soji suka kai ne da jirgi marar matuki.
- Matatar man fetur ta Dangote ta soma aiki
- Tinubu ya naɗa Ali Nuhu Shugaban Hukumar Fina-Finai ta Kasa
A shekaru masu yawa da suke zaune a wannan yanki a Masarautar Ifira a yankin Rigasa ba kowa ne ya san da garin ba ballantana mutanen da ke cikinsa.
Tudun Biri gari ne da ke da kabilu biyu; Hausawa wadanda akasarinsu Musulmi ne sai Gwarawa Kiristoci da suke zaune cikin fahimta da mutunta juna.
Kauye ne da bai wuce gidaje 30 ba a warwatse, sai dai garin yana kewaye da wasu kauyuka irin su Ugara da Sabon Gida da garin Ifira da suransu.
Aminiya ta fahimci a shekaru da dama da kafa kauyen Tudun Biri akasarin mutanensa talakawa ne manoma da ke zaune a gidajen laka.
Kauyen wanda bai fi tafiyar minti 15 ba daga filin jirgin sama na Kaduna, ba ya da ababen more rayuwa kamar asibiti da ruwan fanmo ko na rijiyar burtsasai.
Da ruwan rijiya da kududdufi suka dogara wajen gudanar da ayyukansu na yau da kullum.
Sannan babu makarantar boko ballantana wutar lantarki, babu hanyar mota mai kyau, lokacin damina motoci ba sa shiga garin cikin dadi.
Sannan akwai matsalar tsaro a hanyar zuwa garin, musamman da daddare ko lokacin damina saboda ’yan bindiga da suke sacewa tare da kashe mutane a wasu lokuta.
Wannan ya sa sojojin da ke yaki da ’yan fashin daji a yankin Buruku da Dogon Dawa suke yawan kai samame cikin dajin domin karkabe ’yan ta’addar yankin.
Idan za a tuna, a ranar 3 ga Disamban 2023 ne, jirgin sama marar matuki na sojojin Nijeriya ya jefa bam a kan mutanen kauyen a lokacin da suke taron Maulidi da misalin karfe 9:00 na dare.
Harin bam din da sojojin suka kai wanda daga baya suka bayyana da kuskure, ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutum 100 maza da mata da yara kanana daga garuruwan Ugara da Sabon Gida da cikin kauyen Tudun Biri.
Jama’ar kasa da na kasashen waje sun yi Allah wadai da kisan da ya auku wanda har ta kai gwamnati ga yunkurin sauya fasalin kauyen da rayuwar mutanensa don kwantar masu da hankali a kan bala’in da ya same su.
Haka kuma Gwamnatin Tarayya da ’yan Majaliar Dokoki ta Kasa (sanatoci da wakilai) da wasu manyan mutane sun yi alkawarin biyan diyya tare da sake ginin garin da sauran tallafi da taimako daban-daban a kokarinsu na kai ababen more rayuwa ga mutanen kauyen da kewayensa.
Wasu daga cikin mazauna kauyen sun ce a shekarun baya ’yan bindiga na addabar mutanen kauyen musamman idan suka shiga gonakinsu da ke daji.
Wata dattijuwa a kauyen Comfort Yohana ta shaida wa Aminiya cewa ’yan bindiga suna addabar mutanen garin.
“Amma saboda muna da matasa da maza masu kokari, ba sa iya shigowa cikin kauyen cutar da mu.
“A wasu lokuta suna buge mana mutane mu ma kuma muna sa’ar buge nasu mutanen.
“ Idan suka nemi shigowa garinmu da taimakon sauran mutane da suke kauyukan da ke kewaye da mu, mukan hana su.
“Amma da aka kai wannan harin bam ya halaka mana mazan garin. Sai dai a yanzu jami’an tsaro suna shigowa sosai,” in ji ta.
Shugaban Kiristocin garin Rabaran Sa’idu Musa ya ce tun bayan harin sojin jami’an tsaro suka dan zauna a garin wanda hakan ya sa mutane ke yin barci a natse.
“A baya babu kwanciyar hankali sosai, amma a yanzu muna yawan ganin sojoji a kauyen hakan ya sa muke da kwanciyar hankali,” in ji shi.
Ya ce fatarsu ita ce a samar masu da sojojin dindindin a kauyen tare da yin kira ga gwamnati ta cika alkawarin sake gina garin.
An fara gyara hanyar garin, da gina Massallacin Juma’a
“Yanzu mun samu hanyar mota domin an kankare hanyar motoci na shigowa cikin sauki. Muna fata za a samar mana da ababen more rayuwa kamar yadda aka yi mana alkawari,” in ji shi.
Baya ga hanyar da aka fara gyarawa, a ranar Juma’ar da ta gabata wani babban mutum daga Abuja wanda ba ya so a ambaci sunansa, ya aza tubalin fara ginin Masallacin Juma’a na farko a tsakiyar kauyen.
Masallacin, idan aka kammala zai dauki akalla masallata 2,300 sannan zai zama mahadar al’ummar Musulmin kauyukan da ke zagaye da Tudun Biri.
Wakilin jami’in, kuma dan majalisa mai wakiltar Gundumar Basawa a Karamar Hukumar Sabon Gari a Majalisar Dokokin Jihar Kaduna, Sheikh Muhammad Jamil Abubakar Albani ya ce mutumin da ya fara ginin ya yi alkawari ne a lokacin da ya ziyarci garin bayan harin bam din.
“Abin da ya kawo mu wannan gari shi ne, kimanin wata daya, wani mutum mai daraja mai kima a Nijeriya mun zo nan wajen kuma a ranar ce muka fara Sallar Juma’a a garin kuma wannan bawan Allah ya yi alkawarin gina Masallacin Juma’a a wannan kauye bayan ya yi lura babu Masallacin Juma’ar.
“Cikin yardar Allah ga shi an zo an aza harsashin gina wannan masallaci kamar yadda wannan bawan Allah ya yi alkawari.
“Wannan a wajenmu rana ce mai tarihi wanda wannan gari na Tudun Biri wanda aka kashe bayin Allah suna Maulidi, ba su da Masallacin Juma’a.
“Amma ka san wata jarrabawar sai Allah Ya kawo alheri a cikinta.
“Ga shi za a gina masu masallacin kuma da yardar Allah za a kammala ginin masallacin kafin wata biyu. Burinmu a dauke bakin cikin da ya samu mutanen garin,” in ji shi.
Ya yi wa mutumin da ya fara ginin fatar samun gidan Aljanna, tare da yi masa fatar alheri, inda ya ce Annabi (SAW) ya ce duk wanda ya gina masallaci, Allah zai gina masa gida a Aljanna.
Shugaban Kungiyar Fityanul Islam ta Jihar Kaduna, Sheikh Rabi’u Abdullahi wanda ya halarci wurin aza harsashen ginin ya nuna farin cikinsa da ganin aikin alheri da ke faruwa a garin bayan harin bam din.
“Abin da ya samu wannan gari silar bala’i ne kuma ya zamo alheri na biyo baya sakamakon wannan fitina da Allah Ya saukar a garin.
“Sannan abin farin ciki shi ne wannan gari da aka sani da Tudun Biri Maulana Sheikh Dahiru Bauchi ya canza sunansa da yardar Gwamnan Jihar Kaduna zuwa Tudun Maulidi.
“A da ba su da Masallacin Juma’a sai karamin masallaci, yanzu ga shi a sanadiyar wannan bala’i za a gina musu babban Masallacin Juma’a wanda ko a cikin alkarya ne kadan ne za a samu irinsa.
“Wannan babban alheri ne da ya samu garin,” in ji shi.
Malam Muhammad Sani Musa, Shugaban Munazzamatu Fityanil Islam ya mika godiyarsu ga Allah da Ya sa jarrabawar da ta fada wa garin ta zama hanyar kawo masu ci gaban rayuwa.
Ya ce galibi abubuwan daukaka ba su cika zuwa ba, sai an hadu da wasu abubuwan jarrabawa kuma abin da ya faru a garin ba abu ne mai dadi ba, amma haka kaddarar Ubangiji ta hukunta.
Sai dai akasarin mazauna garin sun ce suna fata gwamnati za samar musu da tsaro kuma ta cika alkawuran da ta yi musu musamman wadanda suka rasa iyalansu da kuma samar musu da karin abubuwan ci gaba domin samun rayuwa ingantacciya.