✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda gobara ta shafe mako biyu tana kone rumbuna a kauyen Bauchi

Mutanen kauyen Siddimari da ke Gundumar Gungura a karkashin Sarkin Buriburi a Karamar Hukumar Ganjuwa da ke Jihar Bauchi sun koka saboda yawan gobara da…

Mutanen kauyen Siddimari da ke Gundumar Gungura a karkashin Sarkin Buriburi a Karamar Hukumar Ganjuwa da ke Jihar Bauchi sun koka saboda yawan gobara da take tashi tana kone musu rumbunan hatsi da dakuna.

Gobarar wadda ta tashi har sau 12 ta kone rumbunan hatsi fiye da 23 a cikin kwanaki goma 14.

Sarkin Buriburi Alhaji Muhammad Bunu Usman wanda ya tabbatar da aukuwar lamarin, ya ce “Wannan bala’i ya damu al’ummar yanki kuma akwai bukatar gwamnati ta kawo agaji don mutanena suna cikin kunci saboda dimbin asarar dukiyoyi da suka yi a gobarar tana da yawa.”

Wani mazaunin kauyen mai suna Malam Garba Muhammad ya shaida wa Aminiya cewa an samu raunin arziki sosai tunda aka shiga cikin wannan jarrabawa “Muna bai wa mutanen da abin ya shafa shawarar su yi hakuri da wannan jarrabawa da Allah Ya aiko musu da ita. Yadda wutar take kamawa takan yi tsalle ne ta tashi kai ka ce wani mutum ne yake tafiya da ita. Wani lokaci takan tashi da tsakar dare wani lokaci bayan Sallar Asuba, wata rana da rana in ta tashi ka ga kamar mutum ne ke tafiya a sama sai ta kama ta zama gobara ta fada kan rumbu ko sito wutar ta tashi, ta kone rumbuna da dakunan adana abinci duk jinkansu ya kone. Akwai ma wani daki abin tausayi in da wadansu almajirai fiye da 200 suke kwana su ma da wutar ta tashi duk kayayyakinsu sun kone kurmus ba abinda aka fitar,” inji shi.

Malam Garba ya ce gobarar ta lalata abincin dabbobi kamar kara da harawar gyada da wake da sauran abincin dabbobi, “Kuma wani lokaci in ta kama kan daki cikin dare, sai an fasa dakin ta baya ake iya ceto mutanen da suke ciki, amma cikin taimakon Allah ba wanda ya rasu sai dai an samu wadanda suka dan ji rauni a kokarin da suke yi na kashe gobarar,” inji shi.

Malam Garba ya ce ana cikin mawuyacin hali domin abincin mutane ya kare sai dai taimakon Allah da zumunci. “Amma saboda yanzu lokacin zafi ne ana kwana ko a gindin bishiya, amma wadansu daga cikin mutanen su yi asara da yawa ya kamata gwamnati ta shigo ta taimaka,” inji shi.

Da yake bayani game da faruwar lamarin, Daraktan Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Bauchi Alhaji Audu D. Isa,  ya ce irin wannan gobara da ke faruwa haka kawai tana faruwa ne a wurare da yawa a cikin jihar, inda wadansu ma suke zargin wai aljannu ne ke sawa. Ya ce a wani lokaci sakaci ke jawo gobarar, inda mutan suke barin kayayyakin wuta ba su kashe ba, idan aka kawo wutar lantarki da karfi wuta ta tashi. Daraktan y ace wata gobarar kuma jarrabawa ce daga Allah, yayin da wasu kuma barayi ke sanyawa don su samu damar yin sata a makwabta.

Ya ce a baya ana samun irin wannan gobara ta bagatatan akwai wadda ta taba faruwa a Unguwar Federal Low Cost da ke garin Bauchi, sai aka kwashe mutanen aka mai da su cikin Unguwar New GRA, kawai ana zaune sai aka ji an ce wut- wuta-wuta har sau hudu ko fiye a lokaci guda. “Ka ga koda sawa wani yake yi ba zai yi wu ya iya sawa har sau hudu ba, a bango sai ka ga wuta tana tashi. Haka akwai wani gari a wajen kauyen Dindima da ke kan hanyar zuwa Yankari in ka shiga Dindima kafin ka kai kan gada yana nan ai karshe sai da aka sa mutanen garin suka bar garin saboda yawan gobara,” inji shi.

Alhaji Abdu ya shawarci jama’a su rika kai rahoton ire-iren wadannan gobara da suke faruwa ga hukumomin da suka dace domin daukar mataki da samun shawarwari.