Hukumar Kididdiga ta Kasa (NBS) ta ce an kara farashin man fetur da dizel wanda har zuwa N707 a gidajen mai a Najeriya.
Hukumar NBS ta ce gidajen mai sun yin karin farashin man dizel da kashi 175.92 cikin 100 daga Naira 273.19 zuwa N654.46 tsakanin watan Afrilun 2021 zuwa watan Afrilun shekarar 2022 da muke ciki.
- Badakalar N287m: EFCC ta tsare tsohuwar Shugabar Majalisar Wakilai, Patricia Etteh
- DAGA LARABA: Yadda Za A Magance Matsalolin Matasan Arewa
“Daga watan Maris zuwa Afrilun 2022, farashin man dizel a gidajen mai ya karu zuwa N539.32, wato kashi 21.35 cikin 100,” in ji rahoton da hukumar ta fitar a ranar Talata.
Tashin farashin fetur
Rahoton ya bayyana cewa farashin man fetur ya karu a gidajen mai zuwa Naira 172.61 a watan Afrilun 2022.
Hakan na nufin karin kashi 3.74 cikin 100 idan aka kwatanta da farashinsa na N166.38 a watan Afrilun 2o21.
“Sai dai kuma farashin ya ragu da kashi 6.85 cikin 100 idan aka kwatanta da N185.30 da gidajen mai suka rika sayarwa a cikin watan Maris,” a cewar hukumar.
Rahoton ya ce mafi tsada da aka sayar da man fetur da gidajen mai shi ne N202.94 a Jihar Kaduna, sai Jihar Enugu N197.51 sannan Jihar Abia N195.27.
Jihohin da aka samu mai mafi sauki su ne Nasarawa da Ebonyi a N165 kowannensu, sai Jihar Legas N165.13 da kuma Jihar Katsina N165.25.
Alkaluman na NBS sun nuna cewa san samu mafi tsadar farashin ne a yankin Kudu maso Gasa a kan N183.69, mafi karanci kuma a Arewa ta Tsakiya a kan N166.57.
Tashin farashin man dizel
NBS ta ce farashin man dizel ya karu daga Naira 273.19 zuwa N654.46, kimanin kashi 175.92 cikin 100 a tsakanin watan Afrilun 2021 zuwa watan Afrilun 2022.
“Daga watan Maris zuwa Afrilun 2022, farashin man dizel a gidajen mai ya karu zuwa N539.32, wato kashi 21.35 cikin 100.”
Alkaluman da rahoton ya fitar sun nuna Jihar da aka sayar da man dizel mafi tsada a watan Afrilu ita ce Osun a kan N707.00, sai Abuja N706.00 sannan Jihar Oyo N704.00.
Mafi saukin da a aka sayar da shi a watan kuma shi ne a Jihar Yobe a kan N535.00, sai johin Kogi a kan N5550.00 sannan Jihar Imo a kan N583.41.
Yankin da man dizel ya fi tsada shi ne Kudu maso Yamma a kan N688.94, sai kuma Arewa maso inda aka fi samun shi da sauki a kan N617.11.