Ranar Litinin Shugaba Muhammadu Buhari ya gana da tsohon shugaban jam’iyyar APC na kasa Kwamared Adams Oshiomhole a fadarsa ta Aso Villa da ke Abuja.
Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Farfesa Ibrahim Gambari, shi ne ya jagoranci Oshiomhole wanda yake sanye da wando da taguwa mai kama da ta jami’an tsaro da ya saba sanyawa har Ofishin Shugaban Buhari.
- Edo 2020: Oshiomhole ya roki gafara
- PDP ta kalubalanci Oshiomhole kan biliyan N42
- Yadda ake shirin dawo da Oshiomhole ya shugabanci APC
Wannan shi ne karo na farko da Oshiomhole ya ziyarci shugaban kasar tun bayan da Kwamitin Gudanarwa na APC da aka kaddamar da kwamitin riko na jam’iyyar bayan rikicin jagoranci da ya mamaye ta.
Aminiya ta tabbatar da cewa ganawar shugaban kasar da Oshiomhole ta tabo batun zaben gwamnan Jihar Edo, wanda za a gudanar a ranar 19 ga watan Satumba.
Zabe na gaskiya
Oshimhole ya bai wa manema labarai tabbaci bayan ganawarsa da Shugaba Buhari cewa jam’iyyar APC ce za ta yi nasara a zaben, ya kuma ce ya nemi shugaban kasar ya samar da tsaro mai inganci a yayin zaben.
Ya kuma ce ya bukaci Shugaba Buhari ya tabbatar an gudanar da tsaftataccen zabe mai nagarta da kuma cikin lumana ta tsari na gaskiya da adalci.
Ya kuma nemi a hukunta duk wanda aka kama yana take doka, ko tayar da zaune tsaye ba tare da la’akari da jam’iyyar da yake goyon baya ba.