✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda fursunoni 3 suka tsere daga gidan yari

Fursunonin sun tsere da sanyin safiyar ranar Asabar.

Wasu fursunoni uku sun tsere daga gidan gyaran hali na Ijebu Ode da ke Karamar Hukumar Ijebu Ode a Jihar Ogun.

Fursunonin da suka tsere sun hada da wani dan fashi da makami da kisan kai, da wani wanda aka yanke wa hukuncin kisa sai wani wanda aka daure kan laifin fyade.

Kakakin ’yan sandan jihar, Victor Oyeleke, ya tabbatar wa Aminiya ranar Talatac ewa, “Lamarin ya faru ne ranar Asabar da misalin karfe uku na safe.

“An tayar da wata tawagar jami’an tsaro dom gano inda suka shiga. Za mu yi aiki da sauran jami’an tsaro don sake kamo su.”

Rundunar So-Safe Corps reshen Ijebu Imushin ta fitar, ta sanar cewa “fursunoni uku da suka tsere daga gidan yari na Ijebu-Ode su ne: Hammed Adeboyejo, Fatai Taiwo Akande da Oguntona Aliu, duk wanda kuka gani cikinsu, ku gaggauta tuntubar ofishin So-Safe Corps da ke kusa da ku.”