✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Fani-Kayode ya hada ni da Nnamdi Kanu — Asari Dokubo

Biyafara za ta kasance karkashin mugun mutum irin Nnamdi Kanu.

Tsohon kwamandan tsagerun yankin Neja Delta, Mujahid Asari Dokubo, ya bayyana yadda tsohon Ministan  Sufurin Sama Femi Fani-Kayode, ya hada shi alaka da jagoran haramtacciyar kungiyar nan ta IPOB masu neman ballewa daga Najeriya.

A wani faifan bidiyo da ya karade shafukan sada zumunta, Asari Dokubo, ya bayyana Kanu a zaman “barawo”, yana mai alwashin murkushe shi.

Sannan ya zargi Kanu da cin moriyar ‘fafutikar’ kafa kasar Biafra kasancewar ba shi da wani takamamman aikin yi.

Ya ce karbi bakoncin Fani Kayode a Gidan Gwamnatin Jihar Bayelsa, da ke Yenagoa, inda suka tattauna kan yadda kungiyar IPOB za ta hada gwiwa da tsofaffin tsagerun mayakan Neja Delta.

“Ya ku ‘yan Biafra, za ku ji muryoyin miyagun mutane suna babatu kan batun kasashen duniya.

“Mun tambaye su ko su wadanne mutane ne suka tallafa musu da kudade, yanzu suna fada mana wai Indiya ce da Rasha. Dan Allah ko haka ake rike kudi da gaskiya yake tafiya? 

“To ina ganin haka Biyafra za ta kasance karkashin mugun mutum irin Nnamdi Kanu.

“Dan ta’addan nan da ake kira Nnamdi Kanu ya yi ikirarin wai sun turo mini kudade ta hannun wani mai suna Omiomio. 

“Ya ce wai sun kawo mini Naira miliyan 20 a Cotonou inda suka damka mini su saboda haka ina jiran su kawo shaidar hakan.

“Sun same ni a Cotonou inda muka hadu; na karbi bakoncin su, na basu masauki da abinci.

“Ko asi ba su zo mini da ita ba sannan kwai mutanen yankin Neja Delta da yawa a lokacin; ba wai ‘yan kabilar Ijaw ne kadai a wajen ba sabanin yadda hoton ya nuna.

“Sai dai suka ci suka koshi sannan suka kuma kwana a otel din da na biya, bayan nan suka shuri takalmansu suka tafi ba tare da sun ba ni sisin kwabo ba,” inji Asari Dokubo.

Sai dai kokarin da Aminiya ta yi wajen tuntubar Fani-Kayode domin jin martaninsa kan zargin ya ci tura.

Haka shi ma Nnamdi Kanu bai ce uffan ba a kan zarge-zargen.

Gabanin Nnamdi Kanu ya tsere daga Najeriya, Fani-Kayode ya kasance daga cikin mutanen da ke raka Nnamdi Kanun zuwa kotu inda ake sauraran shari’arsa a Abuja.