Hukumar Hana Shige da Fice ta Kasa, ta cafke wani mutum kan zargi sace jariri kwana biyar da haihuwarsa.
Jami’an hukumar sun cafke wanda ake zargin ne a ranar Laraba a garin Kalaba na Jihar Kuros Riba.
- Sojoji na shirin ko-ta-kwana bayan ISWAP ta ‘kashe’ Shekau
- Gwamnan Kuros Riba, Ayade ya koma APC
- Za a kashe N805.7m don inganta tsaro a Hedikwatar EFCC
Kakakin Hukumar a jihar, Amor Austin, ya ce “Bayan bincike mun gano safarar yara mutum yake yi.”
Sai dai Mataimakiyar Kwanturola Janar na Hukumar a Jihar, Ijeoma Emenike, ta mika ga sa ga Hukumar Yaki da Fataucin Mutane da Kasa (NAPTIP).
Binciken da suka gudanar sun gano cewar, wanda ake zargin ya sayi jaririn ne da zummar zai fita da shi zuwa kasar waje.
Sai dak hakarsa ba ta cimma ruwa ba, yayin da ya fada a komar jami’an tsaron suka lura jaririn ba dansa ba ne.
Satar kananan yara ko safararsu matsala ce da ke neman zama ruwan dare a Najeriya, sai dai hukumomi na ta kokari yakar masu aikata hakan.