✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dibar-gurya ta jawo wa ’yar shekara 15 matsala

Al’adar dibar-gurya dadaddiyar al’ada ce a kasar Hausa, wadda kusan ta fi shekaru dari ana aiwatar da ita, amma akan samu matsaloli wani lokaci ga…

Al’adar dibar-gurya dadaddiyar al’ada ce a kasar Hausa, wadda kusan ta fi shekaru dari ana aiwatar da ita, amma akan samu matsaloli wani lokaci ga matan da aka aiwatar wa, wadansu kuma sukan dace.
Aminiya ta ziyarci wata yarinya mai suna Atika Umar, ’yar shekara sha biyar a asibitin Maryam Abacha da ke unguwar Tsohuwar Kasuwa a birnin Sakkwato da aka yi wa dibar-gurya, amma ta samu matsala.
A tattaunawar da wakilinmu ya yi da ita cewa ta yi, “Sunana Atika Umar, yanzu shekarata 15, an haife ni a kauyen Ummaruma da ke karamar Hukumar Kware ta Jihar Sakkwato, kuma a kauyen aka aurar da ni. Wannan abin ya same ni ne a watan da ya gabata. dibar-gurya al’ada ce a kauyenmu, an cire wa uwayena da yayyena da abokaina, amma babu wadda ta samu matsala sai ni. Da farko an cire min, sai aka ba da bayanin ba ta yi ba, sai an sake. Aka zo aka sake, sai na samu matsala ta yoyon fitsari, wadda har yanzu nake fama da ita”.
Ta ci gaba da cewa, “Tun lokacin da wannan matsala ta same ni mijina bai guje ni ba, bai canja min fuska ba, kuma yana kula da ni daidai gwargwado har zuwa lokacin da aka kawo ni nan asibiti.”
Madam Deborah Akubo ita ce jami’a mai kula da masu fama da wannan lalura, ta kara haske ga abin da ya shafi wannan yarinya, inda ta ce, “[A ganina] Jahilci da kauyanci ke sanya mutane cikin wannan matsala. Su mutanen kauye da zarar sun aurar da yarinya tana kyamar namiji, sai kawai su ce gurya gare ta, ba tare da sun yi la’akari da yarinyar tasu karama ce ba, kuma ba ta san da namiji ba. Akwai kunya da tsoro, kawai sai su dauki wani ciwo su aza mata, wai shi gurya. Abin takaici kuma bayan sun aza mata wannan ciwon, maimakon su zo da ita asibiti, ba za su yi haka ba, sai dai su kira wanzami su biya shi kudi da sunan ya magance musu matsalar diyarsu, sai ka ga an samu wannan matsalar. Wani lokaci ma har rasa rai ake yi, don almakashin da ake sanyawa ko reza a yanke gaban mace da sunan gurya suna hade, gaban mace ya rika fitar da jini ko fitsari, wanda da wahala ya bari, ka ga an nakasa mace gaba daya. Sai kuma a ce [wai] Allah ne Ya kawo.”
Madam Deborah ta shawarci iyayen yara su daina daukar mataki da kansu, su rika zuwa asibiti, “Wadansu uwayen ma, abin takaici gare su, diyarsu sai ta samu juna-biyu, sai a ce wai za a cire mata gurya. Wane irin rashin hankali ne wannan? Gaskiya akwai bukatar wayar da kan al’ummarmu don su fito daga cikin wannan duhun jahilci.’’ Inji ta.
Alhaji Ahmadu, Sarkin Askin Sarkin Musulmi, shi ne jagoran wanzaman Jihar Sakkwato,  a tattaunawarsa da Aminiya ya ce, “diban-gurya dadadden lamari ne ga al’ummar Hausawa kuma ana yinsa ne tun lokacin da mace take karama kafin ta girma, amma ba kowace mace take da shi ba. Wadda take da gurya a zamantakewar aure ba daidai suke da wadda ba ta da shi ba. Abubuwa uku ne ke fitowa ga farjin mace masu matsala gare ta. Na farko akwai abin da muke ce ma ‘Daba’, idan mace tana da shi, tana girma yana girma, har ya fito waje ya rufe gabanta gaba daya. Don haka shi a waje yake. Akwai na biyu da muke kira ‘Sarka’, [wadda] tana rufe al’aurar mace daga ciki. Sai ta ukunsu ‘Gurya’, wadda ko a littattafanmu an yi maganarta, kuma ta fi shafar mata fiye da sauran”.
Da ya juya kan matsalolin da ake samu wurin cire gurya cewa ya yi rashin amfani da ingantattun kayan aiki ne ke jawo haka, kuma wadansu wanzaman ba su kware ba, sai su je su yi wa yarinya lahani, “Amma idan karamar yarinya ce, muna ba ta maganin da za ta rika amfani da shi har ta girma; babba kuwa da an samu wannan matsalar ba mu san abin yi ba, don akwai wata fata baka cikin gaban mace da zarar aka yi  kuskuren taba ta, to za a samu matsala, sai a samu yoyon fitsari. Don haka ya kamata mutane su san wadanda za su rika kira wurin duba ’ya’yansu, musamman mata. Ita gurya, dan wani tsiro ne da ke fitowa a gaban mace, wanda sai kwararre ke iya cire mata shi. Allah Ya taimake ni ban taba cirewa aka samu matsala ba.” Inji shi.
Aminiya ta kuma ji ta bakin wani magidanci mai suna Malam Murtala ST, wanda ya ce shi gaskiya yana bari a cire wa ’yarsa gurya idan har tana da ita, amma a asibiti, “Domin yanzu zamani ya zo da cigaba, ba kawai mu rika mayar da kanmu wasu gidadawa ba. Ya kamata duk abin da za mu yi mu yi su da gwanaye don gudun samun matsala, ba wai kuma ina sukar uwayenmu wanzamai ba ne.’’ Inji shi.