✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Dan Majalisar Katsina ya tallafawa masu kananan sana’o’i dubu

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta Tsakiya Honorabul Salisu Iro Isansi, ya tallafawa masu kananan sana’o’i da Naira dubu 10 ga duk mai sana’a…

Dan majalisar tarayya mai wakiltar Katsina ta Tsakiya Honorabul Salisu Iro Isansi, ya tallafawa masu kananan sana’o’i da Naira dubu 10 ga duk mai sana’a kimanin mutum dubu.

Dan majalisar ya bayar da wannan tallafin ne da nufin karfafa masu gwiwa don ci gaba da rikon sana’ar maimakon yin watsi da ita saboda karancin jari.

Dan majalisar, ya ce wajibi ne a gare su da taimakawa al’ummar da suke kokarin tallafawa kansu. Don haka ne ya nemi hadin gwiwar Hukumar habaka kanana da matsakaitan masana’antu ta Najeriya (SMEDAN) karkashin jagoranci Dokta Dikko Radda.

Salisu Iro, ya jinjinawa shugaban SMEDAN, saboda irin kokarin da yake wajen hangen nesa da tallafawa masu sana’o’i.

A jawabin, Gwamnan Jihar Katsina Alhaji Aminu Bello Masari, wanda Kwamishinan ruwa da albarkatun kasa Alhaji Musa Adamu, ya wakilta ya ce, tallafawa mai karamin karfi musamman ta fuskar sana’a domin dogaro da kai ba karamin kawo ci gaba bane a tsakanin al’umma domin ta haka ne ake samun ci gaban bunkasar tattalin arziki da kuma rage zaman banza ko dogaro da wani.

Gwamnan ya ce, Dan majalisar ya yi abin koyi musamman ta hanyar kara nunawa jama’a da goyon bayan gwamnati na ganin ta kawar da zaman kashe wando musamman a tsakanin matasa wanda hakan ke je fa su shiga munanen halaye.

Daga cikin wadanda aka tallafawa su dubu da aka ba wannan tallafi na jari, ya hada da mutane biyar-biyar da aka zabo daga kungiyar kurame, masu sana’ar sayar da doya, mata masu yin dillanci da kuma kungiyar Zumunta da ke Dutsin safe da sauran su.