✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda dan ludu ya yi wa yara 12 fyade

An kama wani dan luwadi bayan ya yi wa wasu kananan yara maza fyade a Jihar Sakkwato. Dubunsa ta cika be bayan ya lalata yara…

An kama wani dan luwadi bayan ya yi wa wasu kananan yara maza fyade a Jihar Sakkwato.

Dubunsa ta cika be bayan ya lalata yara 12 a gidan da aka ba shi masauki a kauyen Rikina da ke Karamar Hukumar Dange-Shuni ta Jihar Sakkwato.

“Ba abun da nake ba su saboda nakan yi musu fyade ne idan suna barci amma ba a lokaci guda ba. Idan na yi wa daya yau sai in bari sai bayan sati kafin in yi wa dayan”, inji shi.

Matashin ya shaida wa wakilinmu bayan dubunsa ta cika cewa ya samu damar yin luwadi da yaran ne saboda tare suke kwana a gidan iyayen daya daga cikinsu.

Matsayin mai shekaru 30 daga Jihar Zamfara ya ce shekararsa biyu da wani abokin leburancinsa ya koya masa luwadi kuma tun daga lokacin ya kasa rabuwa da mummunar dabi’ar.

Asirinsa ya tonu ne bayan daya daga cikin yaran ya kama shi dumu-dumu, ya kuma kai kara wajen mahaifinsu.

“Daga nan mutanen unguwa suka mika ni ga ‘yan Hisbah suka kuma ce kar in kuskura in kara zuwa garin”, inji shi.

Daya daga cikin yaran mai shekara 13 ya ce, “Idan na tashi daga barci nakan ji kamar wani ruwa mai kauri a cikin duburata, igiyar wandona kuma a tsinke ko a kwance.

“Na taba kama shi yana kwance igiyar wandona amma na ji tsoron fada wa mahaifina saboda ina ganin ba zai yarda ba”, inji shi.

Mahaifin yaran da aka lalata ya ce, “An ci amanata saboda na dauke shi kamar dan cikina. Na ba shi masauki da abinci har da tufafi, amma irin sakayyar da ya yi mini ke nan”.

Shugaban hukumar yaki da fataucin dan Adam da dangoginsa (NAPTIP) a Jihar Sokoto, Mitika Mafa Ali, ya ce za a gurfanar da wnada ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.