✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda daliban Jami’ar Jos suka kirkiro mota ta amfani da laka da karafuna

Wadansu sun kirkiro makamashin gas daga dusar katako da bawon kwakwa

A yayin da ake ta korafe-korafe kan yadda ba a ganin abubuwan da masana ilimin kere-kere da ke jami’o’in Najeriya da daliban da suke yayewa suke kirkirowa ko kerewa a aikace, wadansu dalibai a Sashin Kere-Kere na Jami’ar Jos, sun samu nasarar kirkiro wata karamar mota da kuma makamashin girke-girke.

Da take zantawa da wakilinmu, daya daga cikin daliban da suka kirkiro mota, mai suna Duru Cynthia Chinonso ta ce, su bakwai ne suka taru suka hada motar. Kuma sun hada motar ce, a matsayin shaidar kundin karatunsu na bara.

Duru Chinonso ta ce sun yi tunanin hada motar ce saboda abubuwan da suka koya a aji ne. Don haka su da suke da sha’awa a fangaren hada motoci suka hada motar. Chinonso ta ce sun fara aikin hada motar ce, a watan Mayun bara zuwa farkon bana.

“Abin da muka kirkiro a motar, shi ne jikin motar wanda muka yi amfani da laka da P.O.P da gam muka fitar da tsarin motar. Kuma muka yi amfani da karafunan da ake jan ruwan famfo.

“Kuma muka yi amfani da injin babur mai kafa uku (Keke NAPEP) da tayoyi da burki da fitilar motar da kasar motar wadanda muka saya a kasuwa.

“Wannan mota tana amfani da man fetur ne, kuma za a iya zuwa ko’ina da ita,” inji ta.

Duru Chinonso ta ce malamansu sun taimaka masu sosai, ta hanyar sanya ido a kan karatun da suke yi, tare da ba su shawarwari a kan wannan aiki da suka yi.

“Ta yi kira ga gwamnati ta rika karfafa gwiwar daliban da suke da sha’awar kirkiro irin wadannan abubuwa.

“Kuma ta samar da kamfanonin da za su rika horar da irin wadannan dalibai a nan gida Najeriya ba sai an fita waje ba.

Dalilin kirkiro motar

“Shi ma da yake zantawa da wakilinmu, daya daga cikin daliban da suka kirkiro makamashin girke-girke na gas, mai suna Khalid Usman Abubakar, ya ce su hudu ne suka kirkiro makamashin girkin a matsayin aikinsu na karatun shekarar da ta gabata.

“Ya ce abin da ya sa suka kirkiro makamashin shi ne sun lura da yadda a yau kusan ko’ina a duniya an ta’alaka ne da wutar lantarki wajen samun makamashi.

“Shi ne muka ga lallai akwai bukatar mu kirkiro hanyar samun makamashi ta hanyar amfani da robobi da dusar katako da fawon kwakwa wadanda ake watsar da su a unguwanni suna gurfata muhalli da yanayi. Don haka muka kirkiro wannan hanya, domin a rika sarrafa wadannan abubuwa,” inji shi.

Khalid Usman ya ce suna hada wadannan abubuwa ne, su kona daga nan sai a samu wannan makamashi na gas.

Ya ce sun yi kamar mako biyu suna gudanar da wannan aiki. Ya ce za iya amfani da wannan makamashi wajen girke-girke da motoci da injinan bayar da wutar lantarki.

Ya yi godiya ga malamansu kan goyan baya da karfin gwiwar da suka ba su, a wannan aiki da suka yi.

Ya kamata gwamnati ta tallafa

Kuma ya yi kira ga gwamnati ta dubi makamashin da suka kirkiro, domin akwai kasashe da dama da suka ci gaba da suke amfani da irin wannan makamashi.

Da yake zantawa da wakilinmu, babban malamin da ke kula da daliban Dokta Ede Godwin ya ce a matsayimsa na wanda ya kula da wadannan dalibai ya yi matukar farin ciki da wannan nasara da aka samu.

Ya ce tuni ake bukatar irin wannan kokari a Najeriya, musamman makamashin girke-girke.

Ya ce makamashin zai taimaka wa ’yan Najeriya musamman mazauna karkara.

Sun samu horon da zai amfane su

Shugaban Sashin Kere-Kere na Jami’ar ta Jos, Injiniya Kamtu Peter ya bukaci a tallafa wa wannan kokari da daliban suka yi.

Ya ce, “Kamfanoni da masu hannu da shuni na Najeriya, su shigo su dauki nauyin wannan aiki. Mu ma za mu tsaya, wajen ganin mun bunkasa wannan aiki da daliban suka yi.”

Shugaban Tsangayar KereKere na Jami’ar ta Jos, Farfesa Danjuma Dajab cewa ya yi, sun horar da wadannan dalibai ne kan abin da zai taimake su. Don haka suka yi wannan kokari na kirkiro wadannan abubuwa.

“A wannan tsangaya da aka bude a shekarar 2014, ba wannan ne karo na farko da dalibanmu suka kere wasu abubuwa ba, akwai dalibanmu kashi na farko da suka kera wasu abubuwa.

“A yanzu ne dai muka fito muka sanar da duniya, domin a san da mu ta hanyar sanar da abubuwan da daliban namu kashi na biyu suka kirkiro,” inji shi.

Farfesa Danjuma ya ce babban burinsu shi ne wannan tsangaya ta zama ta daya a Najeriya a fangaren horar da kere-kere.

Kuma dalibansu su zamo masu dogara da kan su, tare da kera abubuwan da za su kawo ci gaba a Najeriya.

Mataimakin Sakataren Watsa Labarai na Jami’ar Jos, Abdullahi Abdullahi ya ce kokarin da daliban jami’ar suka yi, wani babban abin farin ciki ne ga dukkan al’ummar jami’ar.

“Shugaban Jami’ar Farfesa Tanko Ishaya, ya tashi tsaye wajen ganin daliban jami’ar sun samu natsuwa da yin karatun da za su taimaki kansu da kasa baki daya.

“Don haka zai taimaki daliban don su ci gaba da wannan kokari da suka yi,” inji shi.