✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Coronavirus ke kara watsuwa a Najeriya

In dai ana maganar yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya ne, to za a iya cewa ranakun 26 da 27 ga watan Maris ne suka fi…

In dai ana maganar yaduwar cutar Coronavirus a Najeriya ne, to za a iya cewa ranakun 26 da 27 ga watan Maris ne suka fi muni.

Dalili kuwa shi ne a daren ranar 27 Hukumar Yaki da Cututtuka Masu Yaduwa ta Najeriya (NCDC) da fitar da alkaluma mafi yawa na wadanda ta tabbatar sun kamu da cutar, wato mutum 16.

Da farko dai, da misalin karfe 8.00 na daren, hukumar ta ce an samu Karin mutum biyar wadanda aka tabbatar da cewa suna dauke da cutar; daga bisani kuma, kusan karfe 12 na daren ta ce an sakesamun kari—har mutum 11—lamarin da ya kai jimillar wadanda aka tabbatar sun kamu zuwa 81.

“Zuwa karfe 11.55 na daren 27 ga watan Maris, an tabbatar da mutane 81 sun kamu da COVID-19 a Najeriya—a cikinsu an sallami mutum uku, yayin da daya ya rasu”, inji hukumar a wani sako da ta wallafa a shafinta na Twitter.

Kwana guda kafin nan kuma, wato 26 ga wata, hukumar ta sanar da cewa an samu sabbin kamuwa da cutar mutum 14.

Ban da wadannan ranaku babu lokacin da aka samu adadi mai yawa haka, sai dai ranakun da suka kusa kamo su.

A lokuta daban-daban a ranar 23 ga wata, ta fitar da alkaluman da harba jimillar wadanda suka kamu daga 30 kwana guda kafin nan zuwa 40.

Ma’ana a wannan rana, da kuma ranar 21 ga wata, an tabbatar da mutum 10 a ko wacce rana.

Alkaluma: Hukumar Yaki da Cututtuka MasuYaduwa ta Najeriya (NCDC)

Sabbin kamuwa, sabbin wurare

Kididdiga ta baya-bayan nan da NCDC ta fitar dai ta nuna cewa daga cikin mutum goma 11 da aka tabbaatr sun kamu, takwas a Jihar Legas suke, daya a Jihar Edo, biyu kuma a Jihar Inugu, inda a da babu wanda aka tabbatar.

A yanzu dai alkaluman na nuna cewa Legas ce kan gaba wajen yawan wadanda suka kamu da cutar da mutum 52, yayin da Yankin Babban Birnin Tarayya (Abuja) ke biye mata da mutum 14.

Akwai kuma mutum uku a Jihar Ogun, uku a Jihar Oyo, biyu a Jihar Edo, biyu a Jihar Bauchi, biyu a Jihar Inugu.

Sai kuma jihohin Ekiti, da Osun, da Ribas masu guda daya ko wacce.

Fargabar karuwa

Akwai ’yan Najeriya da ke fargabar cewa adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar zai yi tashin gwauron zabi, musamman saboda ganin cewa ba kowa hukumar NCDC ke yi wa gwaji ba.

Sannan a ranar Alhamis din da ta gabata Ministan Yada Labarai, Alhaji Lai Mohammed, ya bayyana cewa gwamnati na bibiyar mutane sama da 4,000 wadanda ko dai sun dawo daga kasashen waje, ko kuma ake tunanin sun yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun kamu.

Ministan ya kuma koka da yadda ya ce da dama daga cikin mutanen da suka dawo daga kasashen wajen sun bayar da adireshi da lambobin bogi, lamarin da ya sa ake shan wahala wajen gano inda suke.

Wani lamari da ke tabbatar da hakan shi ne wani rahoto daga Jihar binuwai wanda ya nuna cewa wani bawan Allah da ya dawo daga waje ya buya a cikin gidansa, ba a samu gano shi bas ai da makwabtansa suka tsegunta wa hukumomi.

Alhaji Lai ya kuma yi gargadin akwai yiwuwar adadin cutar ta tumbatsa idan ba a yi hankali ba.

Wadanda suka cancanci gwaji

Hukumar NCDC ta ce nau’in mutane biyu ne kawai ake yi wa gwaji don tabbatar da sun kamu ko a’a.

Wadannan mutane kuwa su ne wadanda suka dawo daga kasashen waje (su ma galibi shawara ake ba su su killace kansu sai sun ji wasu alamu sannan su tuntubi hukumar), da wadanda suka yi mu’amala da wadanda aka tabbatar sun kamu.

Masu sharhi dai na ganin kamata ya yi a bude kofofin dakunan biciken da ake gwajin cutar ga kowa tun da ba a san adadin mutanen da suka yi mu’amala da wadanda suka dawo daga kasashen waje ko wadanda su ma suka yi mu’amala da su ba.

A ganin su wannan ce hanya mafi inganci ta taka wa cutar birki a kan lokaci.

Sai dai hukumar ta NCDC ta ce duk wanda ya ji alamun cutar, ko ya ga wanda ya nuna alamun cutar, kamata ya yi ya tuntubi hukumomin lafiya na jihar da yake, wadanda tuni suka sanar da lambonin kar-ta-kwana da za iya kira a ko wanne lokaci.

Daga jihar ne, ko idan abin ya gagara, za a dangana da hukumar ta NCDC.

Me ka iya faruwa?

Hukumomi dai sun ce sun dauki dukkan matakan da suka dace don hana wannan cuta yaduwa a Najeriya.

Ranar Alhamis Shugaba Muhammadu Buhari ya bayyana amincewa da sakin wasu kudade ga hukumar NCDC da kuma asusu na musamman don yakar cutar.

Ya kuma ce ya umarci hukumar ta NCDC ta fadada ayyukants ta hanayr yi wa ma’aikatanta da suka ritaya kiranye, sannan ya ba da umarni ga Rundunar Sojin Sama ta ba da jirage domin kai agaji wuraren da ake bukata.

Tun kafin da ma bayan nan dai wasu jama’a da kungiyoyi da ‘yan kasuwa sun sanar da ba da tallafin kudi don tunkarar annobar.

Gwamnatocin jihohi ma ba a bar su a baya ba, inda wasu suka yanke shawarar rufe kasuwanni da wuraren ibada da sauran wuraren da mutane ke taruwa. Wasu ma har hana jama’a shiga yankunansu daga wasu jihohin suka yi.

Sai dai akwai ’yan Najeriyar da ke ganin wadannan matakai ba su isa ba kuma suna zuwa ne a makare.

A halin yanzu dai zai yi wuya a iya cewa ga abin da ka iya faruwa a mintuna kadan masu zuwa ma balle a kwanakin dake tafe.