✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda cikar madatsar ruwa ta bunkasa noman tumatir a yankin Faskari  

Manoman rani a garin Tafoki da ke Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina suna kara bunkasa noman tumatir bayan samun fadada madatsar ruwa da ke…

Manoman rani a garin Tafoki da ke Karamar Hukumar Faskari a Jihar Katsina suna kara bunkasa noman tumatir bayan samun fadada madatsar ruwa da ke yankin wanda Gwamnatin Jihar ta yi. A bara manoman yankin sun koka a kan yadda karancin ruwa a madatsar ya gaza kai su zuwa watan Afrilu ba, ga shi kuma sun gyara manyan gonaki don yin noman ranin wanda hakan ya tilasta su takaita noman ta yadda ruwan zai kai su ga dabe amfanin da suka shuka.

Wani manomi mai suna Malam Saleh ya ce, tun bara ce suka fara fahimtar fadadar madatsar ruwan da gyaran da gwamnati ta yi wa dam din. Ya kara da cewa, “Mun samu ci gaba ta fuskar noman tumatir duk da cewa farashinsa na yin kasa inda ake sayar da babban kwando Naira 1,300. Mun fadada gonakinmu bisa lura da cewa a yanzu ruwa ya samu fiye da baya, kuma har zuwa yanzu ba mu sayar da kwandon kasa da Naira dubu ba. In kuwa manomi zai sayar da kwandon tumatir daga Naira dubu 1 zuwa sama, lallai za a ce ana samun riba a kai.” Ya kara da cewa, bisa ga samun yawaitar ruwan dam din kimanin shekara biyu da suka wuce, sai a bara ne gwamnatin jihar ta zo ta yi musu yasa  da ’yan gyare-gyare ga hanyoyin da suke ba da ruwan wanda ya taimaka wajen tara ruwa.

Ashiru Shafi’u daya ne daga cikin manoman da ya nuna bukatar gaggawa da suke da ita ta daukar kyakkyawan mataki na gyaran madatsar ruwan ta yadda ko da an samu ruwan sama mai karfi ba zai cutar da dam din ba. “A bara mun fuskanci ambaliyar ruwan sama mai karfi wadda ta zamo barazana ga karamar mafitar ruwan dam din inda hakan na nuni kan bukatar a  dauki matakin gaggawa kafin saukar damina mai zuwa, domin rashin kula zai haifar da lalacewar duk wani gyaran da aka yi har ya kai ga kafewar dam din,” inji shi. Har ila yau, ya kara da cewa, farashin tumatir a kasuwanni ya tsaya yadda yake na tsawon wani lokaci sanadiyar lalacewar kashin farko na gonakin da aka noma a dalilin ruwan saman wanda hakan ya kawo karancinsa a kasuwa. “Kashin farko na noman ranin na tumatirin an shuka shi a watan Oktoba zuwa Nuwamba, amma sai aka samu lalacewar gonaki da dama saboda barnar da ambaliyar ruwan ta yi musu, hakan ne ya sa tumatir ya yi kadan a kasuwa. Wannan karancin ne ya janyo tashin farashinsa ya daga daga Naira dubu 3 zuwa dubu 5 a wannan lokaci kafin faduwar farashin a yanzu inda ya dawo Naira 1,300,” inji Malam Shafi’u.