✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda busa sarewa ta janyo sa’insa tsakanin Sarkin Zazzau da Sojoji

Sojoji sun nemi Fadawan Sarkin su kashe sautin sarewar da ke tashi.

An yi sa’insa tsakanin Fadawan Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmed Nuhu Bamalli da kuma sojoji kan busa sarewa yayin bikin yaye kuratan soji 6,400 da aka gudanar ranar Asabar.

Dambarwar ta gudana ne a Makarantar Horas da Kuratan Soji da ke garin Zariya a Jihar Kaduna.

Sa’insar da ta auku tsakanin bangarorin biyu ce ta sanya Sarki Bamalli ya fasa shiga Makarantar kuma ya koma Fadarsa da ke Zazzau bayan da sojojin da ke gadin mashigarta suka nemi fadawan su daina busa sarewa da bisa al’ada sautinta ke tashin a duk lokacin da wani sarki a kasar Hausa ya bayyana a kowane taro.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, sojojin sun nemi Fadawan Sarkin su kashe sautin sarewar da ya karade wurin, lamarin da fusata Sarkin da tawagarsa kuma suka dauka a matsayin cin kashi.

Sai dai daga bisani, Kwamandan Makarantar, Manjo-Janar Abubakar Ibrahim, ya jagoranci wata tawagar hafsoshin soji da suka je rarrashin Sarkin har gida tare da ba da hakuri.

Aminiya ta ruwaito cewa, yiwuwar hakan ce ta sa Sarkin ya kuma sake dawowa inda ya halarci bikin yaye Kuratan soji.

A Asabar din makon jiya ce ya kamata a gudanar da bikin, sai kuma aka dage zuwa ta jiya domin martaba Babban Hafsan Sojin Kasa, Laftanar-Janar Ibrahim Attahiru da ya rasu sakamakon wani hatsarin jirgin sama da ya rutsa da shi a Kaduna.