✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Buhari ya lashe zaben Shugaban Kasa

Wannan ne zabe mafi muni a tarihin Najeriya – Atiku   Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben Shugaban Kasa da…

  • Wannan ne zabe mafi muni a tarihin Najeriya – Atiku

 

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC ne ya lashe zaben Shugaban Kasa da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata, inda ya samu kuri’a miliyan 15 da dubu 191 da 18, don gudanar da mulki naa wani sabon wa’adi na shekara 4.

Sannan babban abokin hamayyarsa kuma dan takarar Shugaban Kasa na Jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya zo na biyu da kuri’a miliyan 11 da dubu 262 da 978, a fafatawar da ’yan takaran Shugaban Kasa 71 daga wasu jam’iyyu suka yi.

A yayin bayyana wanda ya yi nasarar da ya gudana a cikin dare ranar Talata da ta gabata bayan kammala karbar alkaluman kuri’u daga jihohin kasar nan da aka fara ranar Litinin, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) Farfesa Mahmood Yakubu ya ce ’yan takarar biyu sun samu kuri’un ne daga sahihan kuri’a miliyan 29 da dubu 364 da 209 da a ka kada a yayin zaben.

Shugaba Buhari da Mataimakinsa Osinbajo da matansu bayan miqa musu shaidar lashe zave

Sai dai a yayin bayyana sakamakon zaben wanda ya gudana a Babban Zauren Taro na Duniya da ke Abuja kuma cibiyar tattara sakamakon zaben, daya daga cikin wadanda suka wakilci Jam’iyyar PDP, Mista Osita Chidoka ya bukaci a jingine bayyanawar sai an warware batun korafin jam’iyyarsa na zargin yi mata magudi a wasu jihohi, sai dai Shugaban INEC ya ci gaba da abin da ya fara, bayan ya amsa masa da cewa hukumar za ta waiwayi korafin jam’iyyar tasa a lokacin da ya dace.

Shugaba Buhari ya samu nasara ne a jihohi 19, yayin da Atiku ya samu nasara a jihohi 17 da Babban Birnin Tarayya, Abuja.

Jihohin da Buhari ya lashe sun hada da Ekiti da Osun da Kwara da Nasarawa da Kogi da Gombe da Yobe da Neja da Jigawa da Kaduna da Bauchi da Legas da Ogun da Kano da Katsina da Borno da Sakkwato da Kebbi da kuma Zamfara.

Sannan Atiku ya samu nasara ne a jihohin Ondo da Abiya da Enugu da Ebonyi da Anambra da Oyo da Adamawa da Edo da Benuwai da Imo da Filato da Taraba da Kuros Riba da Akwa Ibom da Delta da Bayelsa da kuma Birnin Tarayya Abuja.

Duk da karuwar adadin wadanda suka yi rajistar zabe kuri’un da Shugaba Buhari ya samu ya gaza wadanda ya samu a zaben shekarar 2015, inda a wancan zaben ya samu kuri’a miliyan 15 da fiye da dubu 400, shi ma Atiku ya gaza samun adadin kuri’ar da Jonathan ya samu a wancan zabe da miliyan daya da rabi. Sai dai duk da haka Buhari ya dara Atiku da kusan kuri’a miliyan hudu. Sama da kuri’a miliyan biyu da rabi da ya ba Jonathan rata a wancan zabe na 2015.

Duka jam’iyyun biyu dai sun ci baya a yawan kuri’un da suka samu a zaben baya. Kuma ga dukan alamu al’adar nan ta amfani da kujerar mulki ba ta yi wani tasiri ga Jam’iyyar APC ba a matakin Tarayya da wasu jihohi, inda Jam’iyyar PDP ta kayar da ita.

Buhari ya samu nasara ce sakamakon gagarumar goyon bayan da ya samu daga yankin Arewa maso Yamma inda ya fito, sai kuma yankin Arewa maso Gabas inda Atiku ya fito da kuma wani bangare na Arewa ta Tsakiya, musamman Jihar Neja.

Jihar da ta fi kawo wa Buhari kuri’u masu yawa ita ce Jihar Kano, sannan sauran jihohin da suka kawo masa kuri’u mafiya yawa a bayanta su ne jiharsa ta Katsina da Kaduna da Borno da Bauchi da Jigawa, kamar yadda lamarin ya kasance a zaben 2015.

 

Zan kafa gwamnatin da za ta kunshi kowane bangare

Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya karbi takardar shaidar samun nasara a zaben na bana, inda ya yi alkawarin cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da kasancewa ta kunshi kowane bangare.

A shekaranjiya Laraba ce aka yi kwarya-kwaryar bikin mika takardar shaidar tabbacin nasara a zaben ga Shugaba Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo wanda aka gudana a cibiyar tattara sakamakon zaben da misalin karfe 2 na rana.

Sai dai wannan yana zuwa ne a daidai lokacin da wanda ya zo na biyu a zaben Atiku Abubakar ya yi watsi da sakamakon zaben inda ya sha alwashin kalubalantarsa a gaban kotu.

Shugaban Hukumar INEC Farfesa Mahmood Yakubu ne ya mika takardar shaidar tabbacin nasarar ga Shugaban Buhari da Mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo.

Shugaban na INEC ya mika musu takardun ne bayan ya yi cikakken bayani a kan dalilan da suka sa ba za a jinge zaben ba kamar yadda Jam’iyyar PDP ta bukata, inda ya ce nauyin korafin bai sa a dakatar da lamarin ba.

Uwargidan Shugaban Kasa Hajiya A’isha Buhari da Uwargidan Mataimakin Shugaban Kasa Misis Oludolapo Osinbajo sun rufa wa mazansu baya, a yayin da jagororin jam’iyyar da suka hada da shugabanta Mista Adams Oshiomhole da Babban Jagoranta na Kasa Alhaji Bola Ahmed Tinubu da sauran shugabanni suka shaidi bikin, da aka watsa kai-tsaye ta kafofin watsa labarai daban-daban.

 

Zaben ya gudana cikin gaskiya da adalci – Buhari

Da yake jawabi bayan ya karbi takardar shaidar nasara a zaben Shugaba Buhari ya ce, “Daga bayanan da masu sanya ido kan zaben na ciki da wajen kasa, ya tabbatar da zaben ya gudana cikin gaskiya da adalci.”

Ya ce, “Yanzu da zabe ya wuce kuma aka bayyana wanda ya yi nasara, wajibi ne mu kalli hakan a matsayin nasara ga Najeriya kasarmu abar sonmu. Don haka a jawabin da na gabatar a yau gabanin wannan na karfafa wa dimbin magoya bayanmu cewa kada su wuce makadi da rawa kan wannan nasara da Allah Ya ba mu, su nuna farin cikinsu ba tare da musguna wa abokan hamayya ba. Dukan ’yan Najeriya masu son ci gaba su mike tsaye cikin ’yan uwantaka domin samar da makoma mai kyau ga kasar nan.”

“Don haka ina tabbatar da cewa za mu ci gaba da jawo dukan bangarorin da suke da cikakkiyar kauna ga kasar nan a zukatansu. Gwamnatinmu za ta ci gaba da kasancewa mai damawa da kowa, kofofinmu za su kasance a bude. Wannan ne hanyar da za mu gina kasar da muke kauna mai cike da zaman lafiya, kubutacciya daga babakere da hadama a tsakanin wadanda aka damka musu amanar dukiyar jama’a,” inji shi.

Shugaban Buhari ya ce zabe ba yaki ba ne kuma bai kamata a dauke shi a matsayin abin a mutu ko a yi rai ba, inda ya yi fatar za a rika daukar harkokin zabe na dimokuradiyya a matsayin gasa.

Ya yi ta’aziyya ga wadanda suka rasa rayukansu ya alla ta hanyar hadari ko tashin hankali a lokacin zaben, inda ya ce zuciyarsa tana tunaninsa suna tare da iyalan mamatan kuma yana addu’ar Allah Ya ba su karfin zuciyar hakurin wannan rashi.

Ya yi alkawarin cewa mutanen Najeriya za su ga kasar da take kara cirawa zuwa mataki na gaba a daidai lokacin da gwamnatinsa take kokarin dorawa daga inda take wajen ceto kasar nan wajen farfado da tattalin arziki da yaki da cin hanci da rashawa. Kuma za a kara wasu muhimman al’amura da aka tabo a lokacin yakin neman zabensa don kyautata al’amuran kasar nan.

Alhaji Atiku Abubakar

Wannan ne zabe mafi muni a tarihin Najeriya – Atiku

A wani taron manema labarai da dan takarar Jam’iyyar PDP Alhaji Atiku Abubakar ya gudanar a Abuja shekaranjiya Laraba, ya ce sakamakon zaben da aka bayyana “gagarumar sata ga bukatun jama’a” kuma ya sha alwashin sai ya kwato “zabensa da aka sace.”

Tsohon Mataimakin Shugaban Kasar wanda ya sha kaye a hannun Shugaba Muhammadu Buhari na Jam’iyyar APC, ya bayyana haka ne a taron manema labarai na duniya da ya kira a Abuja, inda ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben a kotu, yana mai cewa sakamakon zaben wanda ya ba Buhari nasara bai wakilci bukatun al’ummar kasa ba.

“A matsayina na dan Najeriya ina ganin wannan zaben na zamba da INEC ta gudanar ba ya da ingancin da zai samar wa ’yan Najeriya Shugaban Kasa domin ba ra’ayinsu ke nan ba.”

Ya ce da zaben ya gudana cikin gaskiya da adalci zai iya kiran Shugaba Muhammadu Buhari ya taya shi murna kuma yabayr da tasa gudunmawa don tabbatar da ci gaban kasar nan a matsayinsa na gada a tsakanin Kudu da Arewa.

Ya ce dalilin rashin amincewa da sakamakon zabe shi ne kuri’un da Buhari ya samu a wasu bangarorin kasar nan sun wuce kima, ciki har da jihohin Kudu maso Kudu da Arewa maso Gabas da yakin Boko Haram ya addaba.

Ya ce, “Misali a Jihar Akwa Ibom, an samu raguwar yawan rajistar masu zabe da kashi 62 cikin 100 daga zaben shekarar 2015, hatta a inda rajistar masu zaben da wadanda suka karbi katin jefa kuri’a take da yawan gaske a zaben da ya gabata. Wannan kuskuren an maimaita shi a jihohin da PDP ke da karfi kamar Delta da Ribas da Abiya da Benuwai, amma a Borno aka samu karin kashi 82 ciki 100 na rajistar masu zabe. Kai ka ce rashin tsaro kamar baiwa ce a gare su wurin yawan kuri’a.”

Atiku Abubakar ya ce ya yi watsi da sakamakon zaben tare da bayyana cewa shi ne zabe mafi muni da aka taba gudanarwa a Najeriya a cikin shekara 30. “A shekara 30 da na yi a harkar siyasa wannan ne zabe mafi muni da na taba gani a Najeriya. Kuma na gaya wa Janar Abdussalami Abubakar lokacin da ya kira ni cewa hatta zabubbukan da gwamnatocin soja suka gudanar ya fi shi inganci,” inji shi.

 

Zaben ya nuna zabi ne na ’yan Najeriya – INEC

A lokacin da take mayar da martani kan kalaman Atiku, Hukumar INEC ta ce zaben Shugaban Kasar ya gudana cikin gaskiya da adalci.

Babban Sakataren Labarain na Shugaban Hukumar INEC, Mista Rotimi Lawrence Oyekanni ya shaida wa Aminiya a Abuja shekaranniya Laraba cewa, tsohon Mataimakin Shugaban Kasar mutum ne da ake girmamawa kuma dan kasuwar da ya samu nasara da yake da ’yancin bayyana ra’ayinsa.

“Amma a wurin Hukumar Zabe zaben Shugaban Kasa da aka gudanar bana, an yi bisa gaskiya da adalci kuma bisa inganci. Gaskiya ce cewa an samu matsaloli a wasu sassa wanda dama ba a fitar da ran za a iya samu ba, yayin gudanar da irin wannan babban zabe a kasar mai fadi da girma irin Najeriya. Kuma wasu daga cikin kalubalen an same su ne saboda wasu halayen kiyayya na mutanen yankunan. Kuma sakamakon haka ne muka rasa ma’aikacin wucin-gadi daya lokacin da aka harbe shi da bindiga a Jihar Ribas. Kuma wadansu da dama suka samu raunuka,” inji shi.

“Amma zaben ya gudana sumui-lumui a jihohi da dama inda matsalolinsu ba su taka kara sun karya ba. Baya ga haka sakamakon a jihohi da dama ya nuna da bukatar ’yan Najeriya ne hukumar ta fitar a matsayin sakamakon zaben,” inji Oyekanni.

 

Dama ta karshe ga Atiku

Masu fashin baki suna ganin cewa matsayar da Atiku Abubakar ya dauka ta kalubalantar zaben a kotu ba zai rasa nasaba da ganin cewa wannan ita ce dama ta karshe a gare shi ba, da zai iya neman mulkin kasar nan lura da shekarunsa da kuma tsarin karba-karba da akasarin jam’iyyun siyasar kasar nan suka aminta da shi ba.

Tsarin mulkin Najeriya dai ya bayar da damar yin shugabancin kasa sau biyu, don haka da yake Buhari mai shekara 76 ya sake samun nasara, to ba zai sake yin takara a zaben shekarar 2023 ba; domin tilas ya mika mulki. Kuma a bisa tsarin karba-karba da jam’iyarsa ta APC ta yarda da shi, za ta tsayar da dan takara ne daga yankin Kudu a lokacin Buhari ya cika shekara 80 a duniya.

Atiku wanda ke da shekara 72 a halin yanzu, ana ganin zai yi wuya ya sake takara tunda bai kai gaci ba a wannan karo. Kuma tunda bai samu nasara ba yanzu mulki ya kubuce masa ke nan domin bisa ga dukan alamu daga Kudu jam’iyarsa ta PDP za ta dauko dan takararta a zabe na gaba.

Kuma idan mulki ya koma Kudu inda zai dauki shekara takwas a can, to Atiku zai kasance yana da shekara 84 ke nan kafin mulki ya sake dawowa Arewa.

Masu fashin baki suna ganin in har da rai to zai yi wuya ya ce zai nemi mulki a wancan lokaci, don haka ne suke ganin baa bin mamaki ba ne Atiku ya koma ta bangaren shari’a don ya gwada sa’a tunda wannan ne dama ta karshe a gare shi.