✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin Sallah ya gudana a Ibadan

Duk da rashin wadatar kudi a hannun jama’a, al’ummar Musulmi da ke zaune a birnin Ibadan, hedkwatar Jihar Oyo sun gudanar da shagulgulan Sallar bana…

Duk da rashin wadatar kudi a hannun jama’a, al’ummar Musulmi da ke zaune a birnin Ibadan, hedkwatar Jihar Oyo sun gudanar da shagulgulan Sallar bana cikin farin ciki da annashuwa.
Alamar haka ta farko ta bayyana ne kwanaki uku kafin isowar ranar Sallah, a inda aka ga mutane Musulmi da Kirista suna rububin shiga kasuwanni domin sayen kayan abinci da suturun Sallah ga kansu da ’ya’yansu. Alama ta biyu kuma ita ce yawan mutane maza da mata da kananan yara da suka fito kwai da kwarkwata daga gidajensu zuwa filayen Sallar Idi daban-daban da ke cikin birnin na Ibadan.
Limamin Ibadan, Shekh Abdulganiyy Abubakar Agbotomokekere, shi ne ya jagoranci Musulmi maza da mata wajen yin Sallah raka’a biyu da aka gudanar a babban filin Idi na Agodi. Gwamnan Jihar Oyo Sanata Abiola Ajimobi da mai martaba Olubadan na Ibadan, Oba Saliu Adetunji suna daga cikin manyan mutane da aka yi Sallar tare da su. Shi kuwa Ustaz Sani Haruna, shi ne ya jagoranci daruruwan Musulmi ’yan Arewa da suka yi Salla a filin Idi na unguwar Sabo.
Rundunonin tsaro sun girke jami’ansu a filayen Idi daban-daban na birnin Ibadan domin tabbatar da cewa an gudanar Sallar lafiya.
Cikin sakon Sallah jim kadan bayan saukowa daga Idi, Gwamna Abiola Ajimobi ya tunatar da jama’a muhimmancin zaman lafiya, wanda ya ce babu abun da ya fi shi dadin rayuwa. Ya roki dukkan al’ummar jihar da su bayar da gudunmawarsu wajen tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar da kasa baki daya. Ya yi amfani da wannan dama wajen yin kira ga ma’aikatan gwamnati a jihar da su koma bakin aiki, domin da zarar an samu wadatattun kudade to za a biya dukkan ma’aikata albashin da suke bin gwamnati.
Bayanan da Aminiya ta samu daga garuruwa daban-daban a jihohi shida na kudu maso yamma, sun nuna cewa al’ummar Musulmi sun yi Salla ne a shekaranjiya Laraba.