✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda bikin Makarantar Malam Bambadiya ya gudana a Kaduna

Makarantar Malam Bambadiya ta gudanar da bikin cika shekara daya a ranar Juma’a da Asabar 5 da 6 ga Satumba, 2014.An gudanar da bikin ne…

Makarantar Malam Bambadiya ta gudanar da bikin cika shekara daya a ranar Juma’a da Asabar 5 da 6 ga Satumba, 2014.
An gudanar da bikin ne a dakin taro na Jami’ar Kaduna da ke kan Titin Tafawa balewa da ke garin Kaduna.
A lokacin bikin an raba kyaututtuka ga daliban makarantar da suka shiga gasar rubuta gajerun labaran da makarantar ta sanya.
An raba wa wadanda suka shiga gasar kudi da kayayyakin da suka hada da kwamfuta da kyamara da littattafai na kimanin Naira dubu 600.
Farfesa Ibrahim Malumfashi malami a Jami’ar Jihar Kaduna ne ya kirkiro makarantar, inda yake gudanar da darussan da suka shafi koyar da rubuta kagaggun labarai da matakan rubuta waka da wasan kwaikwayo da kuma koyar da nazarin kagaggun labarai a shafin sada zumunci na facebook.
A jawabinsa a wajen taron, Farfesa Ibrahim Malumfashi, ya ce, ya fara tunanin kafa wannnan makaranta ce lokacin da ya shiga facebook.
“Bayan na shiga facebook sai na tsinci kaina a zauruka masu amfani da harshen Hausa fiye da 120, hakan ya sa na ce lallai zan iya ilmantar da mutane ta facebook. Wannan ne dalilin da ya sa muka kafa makarantar Malam Bambadiya domin mu rika ilimantar da junanmu.”Inji shi.
Ya ce: “Marigayi Abubakar Imam ya rubuta littafi mai suna ‘karamin Sani kukumi’, inda ya kawo labarin wata makaranta wadda aka kawo wani malami wanda aka fi sani da Malam Bambadiya, domin ya kula da wani aji kasancewar malamin ajin ya tafi hutu. Da malamin ya zo sai ya yi watsi da hanyoyin da aka tanada don koyarwa a ajin, ya kirkiro nasa tsarin.”
Ya ce, malamin ya yi abin da ya dace daidai da irin yanayin da daliban ke ciki, inda ya rika koyarwa bisa al’ada da addinin Malam Bahaushe, har ta kai dalibai na makukar son sa.
Ya ce, tarihin wannan suna ya wuce iyakar yadda aka kawo  a littafin ‘karamin Sani kukumi’.
“An tambayi marigayi Abubakar Imam game Bambadiya inda ya ce hakika akwai wannan mutumin wanda yake abokinsa a makarantar midil ta Katsina ne…shi ne marigayi Alhaji Ahmadu Kumasi. Wannan malami ya kasance mai amfani da kalmomin Ingilishi masu tsauri duk da cewa bai yi zurfin karatu ba, amma duk kalmar da zai furta ta Ingilshi za ta kasance mai nauyi ce. Shi ya sa abokansa ke masa lakabi da ‘bombardier’, watau mai amfani da kalmomin Ingilshi masu nauyi, masu fasa kai tamkar yadda jirgin yaki ke sakin bom.”
Da yake lissafa nasarorin da makarantar ta samu kuwa, ya ce an samar da littatafai hudu wadanda za a wallafa su nan gaba kadan kuma a kaddamar da su.
Littattafan sun hada da ‘Jamhuriyar Mabarata’ da gajerun labarai a kan mabarata da babban littafin labaran ‘Dare Dubu da daya’ wanda aka soma aikin sa tun a shekarar 1911 ba a kai ga cim ma nasara ba, amma yanzu wannan makaranta na gab da kammala shigar da fassararsa cikin kwamfuta domin bugawa, ta yadda harshen Hausa zai shiga cikin sahun harsunan duniya sama da 100 da aka fassara wannan mashahurin littafin.
A karshe ya yi albishir din makarantar za ta soma gabatar da azuzuwa sabanin yanzu da a intanet kadai ake gudanar da darussa.
Dakta Adamu Ibrahim Malumfashi ya gabatar da makala mai taken: ‘Adabin Hausa Jiya Da Yau: Me Ke Faruwa Da Rubutun Waka Da Zube Da Kuma Wasan Kwaikwayo?”, inda ya yi korafin yadda aka kassara tarihin rubutattun wakoki, aka yi watsi da alkinta wadanda aka samar.
Ya ce:“Misali, an samar da wakokin Wali dan Masani da sauransu tun kafin jihadi, amma yanzu duk sun bace, sai na bayan jihadi aka fi damuwa da su. Ko wakokin masu jihadin da ake zaton an fifita, ai fifita su da karamin mahuci ne. Idan aka cire gagarumar gudunmawar da Bello Said da ta Jean Boyd da kuma B. Mark, su wane ne suka yi fitaccen bincike a kan rubuce-rubucen? Wakokin Maryam, daya daga cikin ’ya’yan Mujaddadi na nan kwance a Jami’ar Landan, ba a tada su barci ba har yanzu.”
Ya zargi mawakan yanzu da rashin akida, inda sukan bugi jaki kuma su doki taiki, sai a ji sun yi wa malam waka, sannan su yi wa mushiriki waka, su yi wa attajiri, su yi wa tantiri, su yi wa sarki, su yi wa musaki.
A game da wasan kwaikwayo kuwa, ya zargi hukumomi da rikon sakainar kashi wajen kula da kuma bunkasa su musamman wadanda akan gabatar a rediyo da talabijin da kuma dandali.
Malam Bukar Mada daga Jihar Zamfara ya zama zakara da labarinsa mai taken ‘kaddara ta riga fata.’ Ya samu kyautar kwamfuta laptop mai dauke da littatttafai (ebooks) sama da dubu biyar. Na biyu shi ne Malam Lawan Muhammad Prp daga Jihar Kano, wanda aka ba shi Naira dubu ashirin da biyar, domin ya sayi kyamarar daukar hoto da littattafai na kusan Naira dubu goma. Na uku a gasar shi ne Bilyaminu Zakariyya Ayagi, shi ma daga Jihar Kano, wanda aka ba shi littattafai na Naira dubu 15.
Daga na hudu zuwa na goma, an ba kowannensu Naira dubu uku, sannan duk wanda ya shiga gasar an ba shi kyautar littattafan da Cibiyar Bukar Usman Foundation da Gidan Dabino International suka bayar.
Mutane talatin da takwas suka shiga gasar, inda za a wallafa labaran daga na daya zuwa na ashirin a littafi mai taken ‘Jamhuriyyar Mabarata’.
Alan Waka da Naziru M Sharif sun nishadantar da taron, sannan an gudanar da wasan kwaikwayo.