Marubutan da aka zaba a gasar Adabi ta kasa sun bayyana burinsu dangane da rubuce-rubucen da suka yi a bikin littattafan da aka gudanar a Jihar Legas a karshen makon da ya gabata.
A lokacin bikin wanda aka yi shi a otel din da ake kira Federal Place da ke unguwar bictoria Island a Jihar Legas, ya samu karbuwa kwarai da gaske, inda wadanda aka zaba suka karanta littattafan da suka rubuta.
Marubutan da aka zaba sun hada da Friday Abba wanda ya rubuta littafi mai suna ‘Alekwu Night Dance’ da Patrick Adaofuyi marubucin ‘Canterkerous Passenger’, sai Soji Cole wanda ya rubuta ‘Maybe Tommorrow’ da Poul Edema da ya rubuta ‘A Plague of Gadflies’ sai Jude Idada da ya rubuta ‘Oduduwa King Of the Edos’ sai Ruth Momodu da ta rubuta littafi mai suna ‘No Fault of Mine’.
Sauran sun hada da Isaac Ogezi da littafi mai taken ‘Under a Darkling Sky’ da Julie Okoh wacce ta rubuta ‘Our wife Foreber’ sai Ade Solanke wanda ya rubuta ‘Pandorad’s Bod’ sai Arnold Udoka wanda ya rubuta littafi mai suna ‘Akon’ sai kuma Sam Ukala wanda ya rubuta ‘Iredi War’.
Wasu daga cikin marubutan da aka zabo da ke zaune a kasashen waje ta hanyar sadarwar Skype sun hada da Farfesa Sam Ukala da Edema da Ogezi da kuma Abba, su ma sun halarci bikin kuma sun karanta ayyukan da suka yi a wurin.
kungiyar ’yan rawa da nishadantar da jama’a ta Afirka wacce ake yi wa lakabi da Crown Troupe of Africa ne suka bude taron da rawa da kida.
Hakazalika fitaccen mawakin nan na Jihar Legas mai suna Aduke ya yi wasa a wurin bikin, sannan wadansu mawakan da masu wasan dabe sun kayatar a wurin.
Da aka tambayi daya daga cikin wadanda suka shiga gasar mai suna Edema ya ce marubuta a Najeriya suna kokari sosai duk da irin kalubalen da suke fuskanta.
Bikin ya samu halartar mutane da dama wadanda suka hada da jaruman Nollywood maza da mata da marubuta daban-daban.
Yadda bikin gasar marubuta ya gudana a Legas
Marubutan da aka zaba a gasar Adabi ta kasa sun bayyana burinsu dangane da rubuce-rubucen da suka yi a bikin littattafan da aka gudanar a…