✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda batun sauya sunan Najeriya ke ci gaba da yamutsa hazo a Twitter

’Yan Najeriya da dama na yin tururuwa zuwa kafafen sada zumunta na zamani domin tofa albarkacin bakinsu kan bukatar sauya sunan kasar zuwa Hadaddiyar Jamhuriyar…

’Yan Najeriya da dama na yin tururuwa zuwa kafafen sada zumunta na zamani domin tofa albarkacin bakinsu kan bukatar sauya sunan kasar zuwa Hadaddiyar Jamhuriyar Afirka (UAR).

Rahotanni sun ce wani kwararre kan harkokin tattara haraji, Adeleye Jokotoye ne ya gabatar da bukatar yin hakan ranar Laraba a gaban kwamitin Majalisar Wakilai kan yi wa Kundin Tsarin Mulkin Najeriya kwaskwarima yayin zamansa a Legas.

Yayin da yake gabatar da kudurin dai, Mista Adeleye ya ce sunan da kasar take amfani da shi yanzu haka na Najeriya Turawan Mulkin Mallaka ne suka yi mata karfa-karfa.

A cewarsa, canza sunan zai kawo gagarumin sauyi na zahiri da ma na halayya kuma zai bude sabon babin ci gaba ga kasar.

Zuwa ranar Laraba dai, maudu’in canza sunan shine ke kan gaba cikin jerin batutuwan da aka fi tafka muhawara a kansu a Najeriya a shafin Twitter.

Wasu dai na ganin yunkurin a matsayin wani mataki na dakile fafutukar wasu masu barazanar ballewa daga kasar.

Har ila yau, wasu kuma da dama na ganin cewa ba canza suna ne babbar matsalar da ke ci wa kasar tuwo a kwarya ba a halin yanzu.

“Yanzu kenan babbar matsalarmu a matsayin kasa ita ce yadda za a canza sunan zuwa Hadaddiyar Jamhuriyar Afirka. Wannan rashin kan-gado ne,” inji Omo Iya Ologi, wani mai amfani shafin Twitter.

Ita kuwa Ayemo Jubar cewa ta yi, “Majalisar Wakilai ta karbi bukatar canza sunan Najeriya zuwa Hadaddiyar Jamhuriyar Afirka. Ku ji fa! Wannan ai wayon a ci ne, wai an kori biri daga bakin dinya.

Shi kuwa Woli Arole cewa ya yi, “Yanzu kenan idan aka canza sunan, idan da ana kiran ’yan Najeriya da Nigerians a Turance, yanzu sai a koma kiransu da Uranium kenan.”