A yau Laraba, shekaru bakwai kenan cif da mayakan Boko Haram suka kai hari Makarantar Sakandiren garin Chibok, inda suka yi awon gaba da dalibai mata 276 a wasu manyan motoci na daukar kaya suka nusa da su cikin dajin Sambisa.
Iyayen ragowar dalibai mata 112 da har yanzu ba a gano ba na Makarantar da aka sace a Jihar Borno, sun ce suna son ganin ’ya’yansu kafin su bar duniya.
Tun bayan sace ’ya’yan nasu da mayakan Boko Haram suka yi shekaru bakwai da suka gabata, wasu daga cikin iyayen sun riga mu gidan gaskiya kamar yadda dabi’a ta rayuwa ta tanadar yayin da wasunsu kuma suka mutu a sakamakon bakin ciki.
Wadanda har yanzu kwanan su ke gaba, suna ci gaba da kyautata zaton cewa ’ya’yansu na raye kuma suna fatan sanya su a idanunsu yayin da suke ci gaba da kiraye-kirayen Gwamnati ta ceto su.
Yayin faruwar lamarin, wasu daga cikin ’yan matan sun samu sa’ar makale wa a jikin rassan bishiyoyi a kan hanyar zuwa dajin inda daga bisani suka samu hanyar komawa gida, galibinsu ba su taki wannan sa’ar ba.
Sai dai bayan haka, wasunsu sun samu nasarar tserewa sannan Gwamnati ta samu nasarar karbo sama da dari daga ciki ta hanyar tattaunawa da maharan.
Wannan lamari na ci gaba da haifar da fargaba ga iyaye musamman ma a Arewa maso Gabashin kasar da ke fama tashe-tashen hankula, lamarin da ya yi tasiri ga harkokin ilimi a Najeriya.
Babu shakka kalilan daga cikin daliban da aka kai Amurka, sun kammala karatunsu na jami’a, sai dai yawancin wadanda suka zana jarrabawar kammala karatun sakandire a nan gida Najeriya ba su yi nasara ba.
Iyayen daliban Chibok 17 sun mutu
Ya zuwa ranar 14, ga watan Afrilun 2016, shekaru biyu kenan bayan da aka sace ’yan matan, an samu akalla mutum 17 daga cikin iyayen daliban da suka riga mu gidan gaskiya, inda galibi bakin ciki ne ya yi ajalinsu saboda sun shafe tsawon lokaci babu amo ballantana labarin ’ya’yansu.
A daidai wancan lokaci ne, gwamnati da iyayen dalibai suka yi taron tunawa da sace daliban a makarantar inda lamarin ya faru.
Daya daga cikin iyayen, Bulama Jonah wanda diyarsa Amina mai shekara 18, tana daga cikin wadanda aka sace kuma yake fatan ganin ’yarsa ta dawo gare shi, ya bayyana takaicinsa dangane da yadda wasu iyayen suka bar duniya ba tare da ganin dawowar ’ya’yansu ba.
A cewarsa, 17 daga iyayen daliban tuni sun riga mu gidan gaskiya bayan faruwar lamarin yayin da dama daga cikinsu sun kamu da rashin lafiya, lamarin da ya sanya ya yi kira ga gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari ta zage dantsenta wajen murkushe ta’addancin Boko Haram da kuma ceto ’ya’yansu.
Bulama ya kuma bayar da sunayen wasu daga cikin iyayen daliban da suka rasu da suka hada da; Stover Mainta, Mainta Yahi, Mutah Sakwa, Haruna Thilaimakalama, Watsai Papu, James Bello, Usman Uffa, Nuhu Mutah, Musa Higwar, Mutah Haruna, Solomi Yama, William Askira, Ali Nkiki, Mary Paul Lalai da Malam Koji.
Sai dai ya ce bai tabbatar da sunayen wasu mutum biyu da ba su dade da mutuwa ba.
“Da a ce gwamnati ta dauki mataki cikin gaggawa, da an ceto ’ya’yanmu domin Amurka ta bayar da rahoton hango wasu ’yan mata 80, amma gwamnati ta gaza ceto su.”
“Da wannan muke kira ga Shugaban Kasa ya kara kaimi wajen ceto mana ’ya’yanmu.”
“Haka kuma, mun ji yadda tsohon shugaban kasa Obasanjo a wani lokaci ya yi furucin cewa, galibin ’yan matan sun samu juna biyu, sannan kuma ya sake cewa ’yan matan sun mutu don ba za a iya gano su ba,” in ji Bulama.