✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda baban Marayu ya zama Sufeto Janar na ’Yan sanda

Jama’a da dama a Lafiya fadar Jihar Nasarawa mahaifar sabon mukaddashin Sufeto Janar Adamu Muhammad sun cika da murna bayan samun labarin nada shi da…

Jama’a da dama a Lafiya fadar Jihar Nasarawa mahaifar sabon mukaddashin Sufeto Janar Adamu Muhammad sun cika da murna bayan samun labarin nada shi da Shugaba Muhammadu Buhari ya yi.

Wannan nadi da aka yi masa ya sanya ’yan uwa da abokan arziki da makwabta, musamman al’ummar Kafor Kaura da ke garin Lafiya yin tururuwa zuwa gidan Alhaji Muhammadu Liman don taya iyalan gidan murna da wannan ci gaba da suka samu.

Gidan iyalan sabon Mukaddshin Sufeto Janar din da ke bayan fadar Sarkin Lafiya ya cika da jama’a masu taya murna kan nadin da aka yi ga Adamu wanda ake yi wa lakabi da Baban Marayu.

Adamu Abubakar ya fito ne daga al’ummar Barebarin Lafiya da mutanen  Jihar Nasarawa ke kira da Kambari.

Aminiya ta zantawa da yayar sabon Sufeto Janar din da suke uwa daya uba daya, Malama Hadiza Muhammadu Liman wacce aka fi sani da Yaya Babba, inda ta ce, “Kanena mutum ne mai gaskiya wanda ya shiga aikin dan sanda don kashin kansa ba don wani ya sa shi ko ya tilasta masa ba, duk da cewa yayansa sojan kasa ne da ya yi ritaya da mukamin Kyaftin. Ya ce yana son ya shiga aikin ne domin ya taimaki kasa.”

Yaya Babba ta kara da cewa, sun rasa mahaifinsu lokacin  Muhammad Adamu yana da mukamin Mataimakin Sufurtanda (DSP), sannan sun rasa mahaifiyarsu lokacin yana da mukamin Mukaddashin Kwamishinan ’Yan Sanda (Deputy Commissioner of Police).

Kamar yadda take bayyana halayensa, ta ce duk da bai tashi a matsayin maraya ba amma ya rumgumin tallafa wa dattawa gajiyayyau da matasa da yara marayu, inda yake biya musu kudin makaranta. Ta ce dalilin wannan hali nasa ne ya sa matasa suka sanya masa lakanin “Baban Marayu.”

Ko a makon ranar Lahadin da ta gabata, yayar tasa ta ce da ya zo yin gaisuwa da addu’ar uku ta rasuwar Sarkin Lafiya, matasa ne suka yi ta binsa suna yi mas kirarin cewa “Sai ka yi IG.” Shi kuma ya yi ta murmushi, “sai kuwa Allah Ya amsa addu’ar marayu, inda bayan kwana biyu kacal Allah Ya yi masa wannan daukaka,” inji ta.

Bugu da kari, ya gina rijiyoyin burtsatse har guda ashirin da bakwai a unguwanni daban-daban a cikin birnin Lafiya.

Babban abokin sabon Sufeto-Janar din, wanda suka tashi tare, Dauda Alhaji Dogara, wanda shi ke rike da sarautar Madakin Wazirin Lafiya, ya shaida wa Aminiya cewa, “mun tashi tare da Sufeto-Janar Adamu Muhammad a Kofar Kaura, a bayan Fadar Sarkin Lafiya. Ya halarci makarantar firamare ta Dunama da ke Lafiya, sannan ya halarci Makarantar Sakandare ta Obi. Bayan ya kammala kuma da ya ci jarabawa sai ya sami gurbin karatu zuwa Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, inda ya sami digiri a fannin Geography sannan ya yi hidimar kasa ta NYSC. Daga nan ya fara aikin koyarwa a karkashin Jihar Filato, kafin a kirkiro Jihar Nasarawa. Ya yi aikin koyarwa na shekaru biyu a Makarantar Sakandare ta Wamba. Bayan nan ne ya nemi a sa masa albarka, domin yana son ya shiga aikin tsaro da gyaran kasa na dan sanda, inda aka sa masa lbarka.

“Da suka yi faretin kammala aikin, an ba shi mukamin Mataimatkin Sufritenda na ’yan sanda (Assistant Supritendent of Police), sanna aka tura shi aiki a kasar Igbo. Na taba kai masa ziyara amma da na ga aiki ya sha masa gaba, na ga ba zai sami lokacina ba, sai na yi maza na dawo gida Lafiya; domin na lura mutum ne wanda ya sa aikinsa a gaba haikan.”

Aminiya ta sami ganawa da kawun Sufeto Janar din mai suna Muhammad Haladu Sarki, wanda ya numfasa ya ce: “Ba mu yi mamaki da wannan mukami da Shugaba Muhammadu Buhari ya ba namu ba, domin mutum ne mai kwazo kan abin da ya sa a gaba. Muna addu’ar zai tabbatar da karuwar zaman lafiya a kasa baki daya, domin gwarzo ne da ya san aiki. Haka ta sa aka rike shi ya yi aiki a Hukumar ‘Yan Sanda ta duniya da ake ce wa INTERPOL har na tsawon shekaru bakwai a kasar Turai, don gaskiyarsa da rikon amana da hana cin hanci da rashawa da hana mummuna aiki, domin ba shi da tabo na halin bera ko da na ko kwabo daya.”

Wakilin Aminiya ya ga matasa da dama a ciki da wajen gidansu suna ta yin murna suna cewa, “Baban Marayu ya sami daukaka, Allah Ya amsa addu’armu.” Matasan sun tabbatar dacew lallai yana taimaka wa tsofaffi da nakassu, da uwa uba marayu da matasa da kudin makarata da kudin aunaka don su yi karatu, su bar zamana kashe wando. Sannan sun ce ya gina rijoyoyin burtsatse da yawa domin mutanen garin Lafiya su debi ruwa kyauta.

Da take bayani game da iyalin dan uwan nata, dattijuwa Yaya Babba ta kara da cewa, Sufeto Janar yana da mata, sannan babbar matarsa ita ce Hafsat wacce aka fi sani da suna Jummai, wacce ya aura a Unguwar Sabon Fegi da ke cikin Birnin Lafiya, sannan daya matarsa ya aure ta ne a wajen jihar, kuma yana da yara.

Aminiya ta zanta da Babban Limamin Lafiya, Sheikh Dalhatu Dahiru, wanda ya ziyarci gidan mahaifin Sufeto-Janar Muhammad Adamu don ya taya su murna da yi masa addu’ar fatan ya sami nasara a sabon mukamin da aka ba shi. Ya ce mutum ne mai gaskiya da kwazo da sanin ya kamata, ta yadda yake tallafa wa jama’a. Ya kuma yi fatan a sami zaman lafiya a kasa baki ba tare da zubar da jini da fitina ba.

Shi kuwa abokinsa da suka yi wasan kasa tare, Dauda Alhaji Dogara cewa ya yi, “ina kira ga ’yan Najeriya da su yi addu’ar samun zaman lafiya, sannan da yin kashedi ga masu ayyukan barna da su shiga taitayinsu, domin sabon Sufeto-Janar ba mutum ne da ke wargi da aiki ba, yana da amana. saboda haka aka rike shi ya yi aiki har na tsawon shekaru bakwai a hedikwatar hukumar ’yan sanda ta duniya da ake ce wa INTERPOL a birnin Lyon na kasar Faransa. Kuma ya yi aikin wanzar da zaman lafiya a kasashe da yawa, don haka ba zai dauki wargi da aiki ba daga manya da kananan ’yan Sanda ko kadan.”

Shi dai sabon Sufeto-Janar na ’yan sanda yana da ’yan uwa da dama, cikinsu akwai soja da dan siyasa da ya taba zama Shugaban Karamar Hukumar Lafiya da kuma wani mai sana’ar sufuri, wanda kuma shi ne shugaban kungiyar masu motocin haya ta Jihar Nasarawa (NARTO) da sauran kanne da dangi da yawa.