✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda Ba’amurke yake koyar da harkokin zuba jari a Musulunci

Farfesa Michael McMillen lauya ne wanda yake zagaye duniya yana koyar da harkar zuba jari bisa koyarwar shari’ar Musulunci. Ya tattauna da wakilinmu a Abuja…

Farfesa Michael McMillen lauya ne wanda yake zagaye duniya yana koyar da harkar zuba jari bisa koyarwar shari’ar Musulunci. Ya tattauna da wakilinmu a Abuja kuma ga yadda hirar ta kasance:
Aminiya: Za mu so mu ji tarihinka da yadda ka fara sanin harkar kasuwanci bisa shari’ar Musulunci sannan kake karade duniya kana koyar da wannan ilimi na Sukuk?       
Sunana Farfesa Michael McMillen ni dan kasar Amurka ne. Kodayake ni lauya ne wanda aiki ya kai ni kasar Saudiyya. A can ne  aka  ba ni kwangilar gina-gine sai aka ce mini za a yi ne bisa tsarin Sukuk wato bisa harkar hadin gwiwa a shari’ar Musulunci. Wannan ya sa na shiga karutu har na tsawon shekara hudu a Saudiyya, sannan na yi shekara biyu a Dubai ina karatu da koyon harkar Sukuk har na fara koyarwa. Kuma a yanzu na kwashe shekara 20 ina koyar da wannan ilimi na yadda ake zuba jari a bisa tsarin shari’a.
Aminiya: Me za ka ce ga wadanda idan an ce wannan tsari na Musulunci ne sai su yi masa wani iri fahimta?
Abu biyu ne abin la’akari a nan. Na farko shi ne wannan tsari ya yi daidai da irin koyarwar addinin Kirista da na addinin Yahudawa. Domin duk sun yi tir da harkar barasa da karuwanci da bayyana tsiraici da naman alade da dai irin wadannan ababubuwa marasa kyau. Babban bambancin shi ne na Ribah wanda shari’ar Musulunci ta yi Allah-wadai da shi. Na biyu shi ne na gina gidaje da kantuna da manyan wuraren ajiye kayayyaki sannan a bayar da su haya don neman kudin shiga.
Aminiya: Me ye tarihin wannan harka a wannan zamani?
An fara wannan harkar ce ta zuba-jari a bisa koyar shari’a a 1970 a kasashen Larabawa wato a Gabas ta Tsakiya sannan abin ya yi sanyi. Daga baya sai kasar Malesiya ta rungumi abin gadan-gadan a 1983 ta kuma mai da shi daga harkar Bankin Musulunci zuwa harkar zuba-jari a Musulunci sannan kasashen Larabawa suka biyo baya suka habbaka shi a 1990.
Aminiya: Yaya aka yi kasar Birtaniya ta riga Amurka shiga wannan harkar ta Sukuk, duk da an san Amurkawa da neman kudi gadan-gadan?
Eh, kasar Birtaniya ta riga Amurka shiga wannan harka. Amma babu banki mai harkar Bankin Musulunci a Amurka, amma Amurka ta sha gaban Birtaniya a harkar zuba-jari a Musulunce fiye da kasashen Turai gaba daya.
Aminiya: Me ye ya kawo haka?
Ijarah wato ladan kudin hayar gidaje da ofisoshi da manyan gidajen aje kaya da sauransu. Sai dai ba kasafai ake sa wannan harka a cikin labarai ba.
Aminiya: Mene ne dalilin da ya sa ba a yayata harkar a kafafen watsa labaran Amurka?
Wannan ya biyo bayan harin aka kai birnin New York na  Amurka a shekarar 2001 wato 9/11 domin wannan hari ya sa wasu Amurkawa sun tsani Musulmi. Amma muna ginawa da saye da ba da hayar gidaje da shaguna sannan mu kara zuba jarin a kasashen Larabawa.
Aminiya: Mene ne tarihi da matsayin Sukuk a Afirka?
kasar Aljeriya da Afirka ta Kudu suna yin wannan harka ta Sukuk sannan na kwashe shekarar da ta wuce ina koya wa Babban Bankin kasar Tanzaniya yadda zai fara Sukuk a birnin Dar es Salaam da kuma tsibirin Zanzibar wanda yawancin mutanensu Musulmi ne. Har ila yau, akwai kasashe da yawa wadanda suke shirin fara wannan harka.
Aminiya: Ko akwai wadanda ba Musulmi ba wato Kiristoci da sauransu wadanda suka shiga wannan harka?
Akwai su sosai. Domin ita harkar kasuwanci ba ruwanta da addinin mai saye ko na mai sayarwa. Kuma manyan kamfanonin Inshora na Amurka suna harkar don harka ce mai inganci. Don an aje kudin adashin gata na ma’aikata, don haka ne suka sa wannan dimbin kudi a Sukuk.
Aminiya: Wace shawara za ka ba ’yan kasuwa da masu zuba jari don su rungumi wannan harka su kwashi garabasa?
Abin da nake so a lura da shi shi ne kamfanonin ’yan kasuwa su rika harkar Sukuk wato su saya su sayar. Najeriya babbar kasa ce wacce tana da tanadin kwarai kamar yadda take da tsarin mulki da ke kare yadda za a raba kadarori idan kamfani ya durkushe da karbar takardar mallakar kadara kamar gida kafin a ba mutum bashi mai girma wanda babu irin wannan tsari a kasashen Gabas ta Tsakiya. Ya dace ’yan Najeriya su kara himma don su karu da Sukuk.
Aminiya: Wane kira za ka yi ga ’yan Najeriya game da zuba jari a gida maimakon kasashen waje?
Shi dan kasuwa yana zuba jari ne inda yake hasashen zai samu riba. Sannan da kasar da ke da zaman lafiya. Wace ta fi gaba kan harkar Sukuk ita ce kasar Saudiyya sannan mutane daga kaseshen duniya suna saye. Duk mutumin duniya na son kudi (dariya).
Aminiya: Ko kana ganin Sukuk zai danne harkar banki irin na Turawan Yamma?
A yanzu dai Sukuk na bayan bankin ’yan jari-hujja, amma abu ne da zai iya faruwa. Sai dai a yanzu suna tafiya kafada-da-kafada. Duk da bankunan ’yan jari-hujja sun fi na Sukuk karfin jari. Sannan idan akwai zuba jari da yake da kasada matuka, sai an hada da bankin Turawa don idan ba haka ba sai hukumomi su hana harkar.bbb