Kishi kumollon mata aka kuma mace wacce bata kishin mijinta jaka ce.
Lallai na san babu macen da za ta so a kira ta jaka sai dai kash, wasu matan kishin nasu yak an kaisu ga hallaka duniya da lahira. Ga wadannan mata da zan bada labarinsu kan kishi, lalle sun kira ruwa da ya wuce da su sai dai da me, Allah Ya sa sauran mata su dauki darasi ga wadannan labaran.
Mace ta farko dai babu abin da ta tsana kamar kishiya saboda haka da ta samu labarin mijinta zai yi aure sai ta shiga ta fita, ba ta malam ba ta boka don ta ga cewa auren bai yiwu ba, amma kuwa Allah Ya riga Ya yanke hukuncinSa tun kafin a hallice ta kuma ta kasa fahimtar babu wanda ya isa ya hana Allah ikonSa. Maigida dai ya yi aure, maimakon ta rungumi kaddara, uwargida ta ci gaba da abin da ta saba. Ba a jima ba, amarya ta fara ciwo babu hmm, babu hmm-hmm babu kuma motsi. Ana ta jinya tsawon lokaci amma tana nan a hakan sai kawai uwargida ta kwanta ciwo ashen na ajali ne. Allah Ya dauki ran uwargida sai bayan kwanaki kadan a ka shiga dakinta aka fara hada kaya. Mutuwa mai tonan asiri sai kawai ‘yan’uwanta suka ga ‘yartsana a karkashin gadonta an daddaureta, suka fara warwarewa sai kawai suka ji an sa ihu daga waje cewa amarya ta fara motsi suka fito da gudu don gani wa idanuwansu. Jama’ar gida suka gansu da ‘yartsana a hannu suna warwarewa. Gama warwarewar ke da wuya sai kawai amarya ta mike kamar ba ita ta ke ciwon ba. Daga karshe ta samu lafiya garau sannan ta ci gaba da hayayyafa wa maigida.
Ta biyun kuwa nakuda ce ta kama ta a unguwa aka kai ta asibiti sai kishiyoyinta suka bude dakinta don su kai mata kayan jariri asibiti, suna duba karkashin gado sai ga dan karamin mutum mutumi an daddaure shi, suka dauka suka kona ba su fada wa kowa ba. Aka kira maigida cewa tana asibiti, sai kawai ya yi masu ihu cewa to sai me? A kanta aka fara haihuwa? Wannan abun ya ba su mamaki don kuwa su ukun ba su da sakat idan abu nata ne, komai bare-bare yake don kar ya bata mata rai.
To uwargida, idan kunne ya ji, jiki ya tsira. Amma idan a kika bi son zunciya, a juri zuwa rafi, wata rana tulu fashewa zai yi. Babban abun shi ne, Allah Yana nan a madakata Yana jira, ko ba-jima, ko ba-dade sai asiri ya tonu. Ni mamaki na shi ne me zai sa mutum ya sayar da lahirarsa saboda mutum dan’uwansa? Shi dai Allah Ya umurce mu da aure don ya kasance hanyar tsira a gare mu, amma saboda son zunciya da wawanci irin na wadansu matan sai su maida aure hanyar shiga wuta saboda dai kawai su zauna su kadai ko su kasance su zama sune masu cewa a yi ko a bari.
Ni a gani na akwai hanyoyi mafi sauki idan mace ta rike su za ta samu rabo nan duniya kuma ta samu a lahira. Amma idan mace ta dogara da cewa dole sai ita ko kuma tana son ta ga wata a cikin kunci saboda wannan tana zaman bautar aure, lallai ta san cewa Allah ba azzalumin kowa ba ne kuma idan Ya ga dama ya ba ta sa’a ta kankanin lokaci daga baya asirinta ya tonu ko kuma Ya yi ta ba ta sa’a har karshen rayuwarta inda daga karshe ta zama abin tausayi. Ko kuma ta kasa samun sa’ar nan duniya, ga zaman kabari mai wuya na jiranta. Haba, ai ya kamata mata mu yi wa kanmu karatun tanatsu. Allah Ya tsare mu da son zunciya.
Ku biyo mu a wannan shafi, ku ji yadda mace za ta iya sace zunciyar mijinta a tsanaki, ga riba nan duniya, ga kuma riba can lahira. sannan yin wadannan abubbuwa za su kasance kariya gare ta da izinin Allah daga sharrin kishiya makira.