Tsohon zakaran damben boksin na duniya ajin babban nauyi, Anthony Joshua ya soma dawo da martabar wasansa bayan ya doke dan wasan damben Amurka Jermaine Franklin sau biyu a jere a Landan a ranar Asabar.
Anthony Joshua ya soma fafutikar dawowa kan ganiya yayin da ya yi iya kokarinsa domin ya samu nasara a wannan damben saboda ya dawo da martabar dambensa da yake neman rasawa.
- Dalilin da Shugaban NNPP na Kasa ya yi murabus
- Na shafe wata daya ban ga Tinubu ba — Wanda ya je Legas a keke
Wannan ne karon farko da Joshua ke samun nasara a dambe bayan ya sha duka a hannun Oleksandr Usyk har sau biyu.
Damben wanda aka kara shi a gaban ’yan kallo 2000, shi ne wanda dan damben mai shekara 33 ya kara yi tun bayan da ya sha duka a hannun zakaran Ukraine mai kambunan WBA da IBF da WBO da IBO wato Oleksandr Usyk.
Haka kuma wannan ne kuma karon farko da ya samu nasara a dambe a sama da shekara biyu, wanda hakan ke nufin a tarihin dambensa, ya yi nasara sau 25 an kuma yi galaba a kansa sau uku.
Alkalai ukun da suka yi alkalancin damben bakinsu ya zo daya a irin makin da suka bayar wanda hakan ya kai Joshua ga yin nasara.
Makin da da suka bayar shi ne 118-111 da 117-111 sai kuma 117-111.
Ga Franklin kuwa mai shekara 29, wannan ne karo na biyu da ake doke shi bayan da Briton Dillian Whyte ya yi nasara a kansa a Nuwamba.
Irin naushin da Joshua ya soma kaiwa da farko da alamu ba su da wani karfi, wanda hakan ya sa Franklin mai shekara 29 ya soma samun karfin gwiwa, inda har ya rinka gwalo ga abokin damben nasa wanda ya fi shi tsawo.
Joshua, wanda jini ya rinka fitowa daga hancinsa tun da farkon fara damben, amma duk da haka shi ya yi nasara.
Buhari ya taya Joshua murna
Shugaba Muhammadu Buhari ya yaba da nasarar da dan wasan damben Birtaniya kuma haifaffen Najeriya ya samu kan abokin karawarsa Jermaine Franklin a karawar da suka yi a filin wasan dambe na O2 Arena da ke birnin Landan.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Tuwita Shugaba Buhari ya ce nasarar da Joshua ya samu ta nuna cewa ta hanyar aiki tukuru da sadaukarwa da jajircewa ne ake samun nasara.
Shugaban Buhari ya yi fatan nasarar ta kasance daya daga cikin nasarorin da ba za a taba mantawa da ita ba a tarihin gasar dambe.
Nasarar ita ce ta 25 da Joshua ya samu tun bayan zamansa fitaccen dan wasan dambe a shekarar 2013.