Daruruwan `yan Boko Haram da iyalansu sun tsere daga maboyarsu zuwa gefen dajin Sambisa da ke Borno, sakamakon ambaliyar ruwa.
Aminiya ta gano yadda `yan ta`addan 7o suka nutse a ambaliyar, yayin da wasu 200 har da Kwamandodji biyar suka rasa rayukansu, sakamakon ruwan wutar da jiragen yakin soji suka yi musu a karshen makon da a gabata.
- NAJERIYA A YAU: Mai Yiwuwa A Fuskancin Matsanancin Wahalar Mai Kwanan Nan A Arewacin Najeriya
- ’Yan bindiga sun kama ‘barawo’ a Katsina, sun mika shi ga hukuma
Binciken har wa yau ya gano cewa a safiyar ranar Lahadi ne ambaliyar ta auku a tabkin Yedzaram, inda ta lakume sansanonin `yan ta`ddan da ke kauyukan Shehuri, da Kumshe, da wani yanki na Gaizuwa .
Baya ga amabaliyar kuma, karancin makamai, da abinci ma na daga dalilan tserewar ta su.
A hannu guda kuma, wani Kwamnadan kungiyar Goni Farooq ya mika wuya ga rundunar sojin a Karamar Hukumar Bama da ke Jihar Borno a ranar Lahadi.
Wata majiyar sirri ta bayyana cewa Kwamnadan ya kuma mika makamai da suka hada da AK47 45, da harsasai, da manyan bindigogi, da na`urar samar da lantarki mai amfani da hasken rana, da sutura da sauran kayayyaki.