Shataletalen Baban Gwari da ke birnin Kano ba boyayyen ba ne ga duk mazauna birnin da kewaye, musamman yankunan kofar Ruwa da Kurna da Rijiyar Lemo da Bachirawa.
Yana kan babbar hanya ce da mutane da dama ke bi ciki har da jami’an gwamnati, domin hanya ce da ake bi domin zuwa ko dawowa daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano.
- Bello Turji ya rungumi zaman lafiya – Gwamnatin Zamfara
- NAJERIYA A YAU: Gaskiyar Batun Kyautar Motocin Yakin Najeriya Ga Kasar Nijar
A duk lokacin da aka yi ruwan sama mai yawa, al’ummar wannan yanki sukan shiga fargabar yadda za su samu hanyar da za su wuce domin fita da komawa gida.
Binciken Aminya ya gano babu gwamnatin da ba ta yi aiki a wajen ba, amma har yanzu ba a samu nasara ba.
Gwamnatin Jihar Kano a karkashin Dokta Abdullahi Umar Ganduje ma ta sha gudanar da aiki a shataletalen, inda ko a daminar bana Ma’aikatar Muhalli ta kaddamar da shirin yashe magudanun ruwa, inda da shataletalen ta faro, amma duk da an samu ambaliya ruwa kusan sau hudu a wajen.
“Duk lokacin da aka ce damina ta zo gaskiya muna murna domin za a yi noma. Sai dai muna shiga kunci idan muka tuno cewa wannan waje yana fama da ambaliya. Idan ana ruwa to nakan hakura da sana’ata domin kuwa ruwa yana malalowa har inda nake sana’a,” inji wani mai gasa kifi, Bashir Ibrahim (Tola).
A zantawar Aminya da wani mazaunin wuri, Malam Aminu Tudun Wada ya ce, daga cikin abubuwan da suke haifar da ambaliyar akwai yadda masu sababbin gine-gine a kan hanyar suke rage fadin magudanar ruwan.
Ya ce, matukar ba za a fadada magudanar ruwa ba, to wannan waje ba zai rabu da ambaliya ba.
“Waje ne da yake a kwari kuma ya dade a haka. Amma da can yana da magudanun ruwa masu fadin gaske, amma an yi gine-gine an rage fadinsu, wasu ma sun toshe. Dama can yana da kwalbatinsa da aka gina tun 1975.
“Ina tabbatar maka cewa, a duk lokacin da muka ga ana gyara a wannan waje to fa mun san ba inda zai je domin babu irin gyaran da ba a yi ba a baya. Ba wai ya tsaya a iya wurinmu ba ne, babbar hanya ce har zuwa Katsina da Jamhuriyar Nijar,” inji shi.
Shi ma wani mai matukin A Daidaita Sahu, Bashir Usman ya ce a duk lokacin da ake ruwa ba ya bin hanyar domin ya san ba zai iya wucewa ba.
Ina mafita?
Da yake bayyana hanyar da za a iya magance matsalar, Alhaji Aminu Tudun Wada mai kimanin shekara 70 ya ce, “A bude kwalbatin da aka toshe wanda ya biyo ta tsakiyar titin da yanzu haka gwamnatin jihar ke yi.
“Wannan aiki idan aka kammala shi za a gyara matsalar da kusan kashi 60. Na biyu a daga shataletalen domin ya fada kwari lura da gine-gine da ake yi a wurin.”
Jami’in Hulda da Jama’a na Ma’aikatar Muhalli ta Jihar Kano, Sunusi kofar Na’isa ya ce tuni suka fara aiki domin magance matsalar.
Ya ce, tsawon shekaru suna gudanar da ayyuka da dama da suka rage ambaliyar da kaso mai yawa.
“A yanzu haka Ma’aikatar Ayyuka tana gudanar da aikin samar da magudanar ruwa wacce za ta bi ta tsakiyar titin zuwa Filin Jirgin Sama. Wannan aiki idan aka kammala shi zai kawo karshen wannan matsala baki daya,” inji shi.