✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ambaliya ke neman kawo karancin abinci a Najeriya

Farashin kayan abinci na hauhawa kuma matsalar tsaro ta hana yin noma a wasu sassa

Najeriya na fargabar shiga karancin abinci a Najeriya sakamakon yadda ambaliyar ruwa ke lalata gonaki da amfanin gona a sassan kasar.

Ambaliya ta ja wa dubban manoma wadanda akasarinsu manoman shinkafa da masara ne a jihohin Kebbi, Bauchi, Zamfara, Sakkwato, Kwara, Ribas da Kuros Riba da sauransu, a asarar abin da noma.

Hakan ya kawo fargabar hauhawar farashin kayan abinci kamar yadda binciken Aminiya ya nuna tuni farashin kayan abinci suka fara tashi a kasuwanni.

Alal misai buhun masara a Kano N20,000 ne, a Binuwai kuma N22,000; Abuja kuma ana sayarwa N24,000, sai Legas N25,000. A tsawon shekarar da ta gabata farashin buhun masara N9,000 zuwa N1000 ne.

Ita kuwa shinkafa ‘yar gida yanzu buhunta N55,000 ne a Kano amma a Abuja ta kai N58,000. Babban buhun wake kuma ya kai N22,000 zuwa N24,000 a jihohi.

– Jan kunne –

Tun da farko hukumar kula da yanayin ruwa (NIHSA) ta ce ruwan da ya taru a Kogin Neja na barazanar ambaliya a jihohin Kebbi, Neja, Kwara, Nasarawa, Kogi, Anambra, Delta, Edo, Ribas da kuma Bayelsa wadanda kogin ya keta su.

NIHSA ta kuma yi hasashen fara samun ambaliya a Najeriya daga 6 ga watan Satumba a Jihar Kebbi, kamar yadda Darakta-Janar na hukumar, Clement Onyeaso Nze ya bayyana.

Tuni aka samu mummunar ambaliya a jihar Kebbi da kuma Zamfara, Sakkwato, Neja , Bauchi, Kwara, Kuros Riba da kuma Ribas.

Lamarin ya haifar da babbar damuwa musamman ganin yadda ambaliyar ta share hekta dubu dari biyar na gonaki da amfanin gona a Jihar Kebbi.

– Asar da manoma suka yi–

Hukumar agaji a Jihar Kebbi wadda ke kan gaba wajen noman shinkafa a Najeriya ta ce ambaliyar ta share hekta 450,000 na gonakin shinkafa sai kuma hekta 50,000 na sauran kayan da aka noma.

An yi kiyasin cewa asarar da manoma suka yi a Jihar Kebbi ta haura Naira biliyan biyar.

Wata manomiyar shinkafa a Jihar, Lubabatu Bunza ta ce ta yi asarar abin da ta noma a gonarta mai fadin hekta 16,000 a ambaliyar.

Malam Isha Ahman, manomi a Karamar Hukumar Patigi, Jihar Kwara ya ce ambaliya ta share gonar da ya shuka shinkafa hekta shida da kuma masara hekta hudu a farkon watan Agusta.

Manoman da suka ce sun karbi rance ne daga bankunan kasuwanci domin yin noma, sun ce asarar da suka tafka ta sa da kyar za su iya biyan basukan da suka ci.

Yawancin manoman da ambaliyar ta shafa a Jihar Kebbi sun ce sun karbi rance ne daga shirin noman shinkafa na Anchor Borrowers na Babban Bankin Najeriya, kuma da wuya za su iya biya saboda irin asarar da suka tafka.

– Akwai babbar barazana–

Shugaba Kungiyar Manoma ta Najeriya (AFAN) Ibrahim Kabiru ya ce ambaliyar ta fi shafar gonakin shinkafa da dawa da sauran hatsi.

Ya ce ko da yake da wuya a iya hakikance iya barnar da ambaliya ta yi a fadin Najeriya, amma babbar barazana ce ga samuwar abinci, musamman kasancewar matsalar tsaro a kauyuka ta hana manoma zuwa gonakinsu.

Wani masani kan wadatuwar abinci Mathew Ajayi ya ce Najeriya ta kusa fadawa cikin matsalar karancin abinci idan aka yi la’akari da yadda farasin kayan abinci ke tashin gwauron zabo a kasar.

“A bayyane yake cewa muna dab da shiga babbar matsalar karancin abinci duba da hauhawar farashin kayan abinci a kasar.

“Ga shi yanzu ambaliya na ta lalata gonaki sannan ’yan bindiga sumn hana manoma zuwa gonaki’’, inji masanin.

Wani manomi kuma mai kamfanin casar shinkafa a Jihar Neja, Alhaji Mukhtar Umara ya ce za a iya samun karancin shinkafa saboda ambaliyar da kuma ’yan bindigar da suka tilasta wa manoma tserewa su bar gonakinsu.

“A iya sanina manoma da dama sun noma shinkafa bana amma ruwa ya tafi da abin da suka shuka.

“Manoma da yawa kuma ba su iya zuwa gona ba musamman a nan Jihar Neja”, kamar yadda ya bayyana wa wakilin Aminiya ta waya.