Assalamu alaikum warahmatullah, da fatan kuna cikin koshin lafiya.
A yau na zo muku ne da yadda ake yin ‘banana smoothie’ cikin sauki.
- Abubuwan hadawa:
- Ayaba
- Madara ta ruwa
- Flavor
- Yadda ake hadawa
- To da farko za a bare ayaba a tsaga ta a cire bakin abin da ke tsakiyarta.
- Daga nan sai a yayyanka ayabar a sa a blender a nika.
- Sai a zuba madara da ‘Flavor’ daidai bukata a cikin nikakken ayabar sannan.
- Bayan nan sai a juye a mzubi a sa a firji ya yi sanyi.
A sha dadi lafiya.