✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake yin mashe

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin mashe. Mashe abinci ne mai…

Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan alheri kuma ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku yadda ake yin mashe. Mashe abinci ne mai kama da masa amma ya fi masar kankanta sannan abubuwan da ake amfani da su wajen sarrafa shi daban yake da na masa ko waina. An fi cin wannan irin abincin ne a kasar Hausawa domin  karyawa da safe. Sannan mafi yawanci sun fi son cin sa da yajin kuli-kuli ko kuma yajin barkono. A sha karatu lafiya.

Abubuwan da ake bukata

·        Garin gero

·        Man gyada

·        Magi

·        Yis

·        Flawa

·        Gishiri

·        kuli/yaji

Hadi

A samu gero sannan a wanke a cire tsakuwa a busar sannan a kai a nika ba tare da an saka kayan kamshi ba ko kayan yaji. Bayan haka, sai a tankade wannan garin sannan a sa a roba sai a samu garin flawa a zuba a ciki a gauraya su gaurayu sosai. A duma ruwa sannan a zuba yis a ciki idan ya dan tashi, sai a zuba a cikin hadin garin gero da  flawa.

A samu ruwa ana zubawa ana kwaba hadin har sai ya yi kauri kadan. Hadin ya kasance ba mai kauri sosai ba sannan a rufe a sanya a rana har sai kullun ya tashi.

Sannan a dora tukunyar tuya a wuta a zuba man gyada da albasa su soyu. Sai a dauko kullun ana yankawa da ludayi ko cokali daidai girman da ake so ana soyawa kamar yadda ake tuyar fanke sannan a kwashe.

A samu yajin kuli mai dauke da magi a ci da shi ko kuma yaji mai dauke da magi ana dangwalawa ana ci.