✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake yin kunun goruba

Jama’a Assalamu Alaikum, barkanmu da warhaka. Yau kuma ga mu dauke da yadda ake yin Kunun Goriba.

Jama’a Assalamu Alaikum, barkanmu da warhaka. Yau kuma ga mu dauke da yadda ake yin Kunun Goruba.

Kayan da ake bukata

– Garin goriba

– Gero

– Sukari

– Citta

– Kanumfari

Kunun goruba
Kunun goruba

 Yadda ake hadawa

– A surfa gero a shanya shi ya bushe, sai a tankade shi a fitar da dusar, sai a wanke tas a zuba citta da kanumfari a markada.

– A tace markaden da rariya yadda ake tace kunu.

– A tafasa garin goriba yadda ake tafasa tsamiya, a bari ya yi dan kauri sai a sauke, a tace ruwan a cire tsakin.

– A bari ya dan sha iska sai a dama sauran kunun a juya sosai sai a zuba sukari.

– A zuba a gora sannan a saka a firinji.

Wannan yadda ake yin kunun goriba ke nan.