Wani gungun ’yan jam’iyyar APC na kokarin maido da dakataccen Shugaban jam’iyyar, Adams Oshiomhole kujerarsa.
Babban Darektan Kungiyar Gwamnonin Masu Yunkurin Kawo Ci gaba (PGF), Salihu Lukman Mohammed, ya bayyana haka a wasikarsa ga shugaba jam’iyyar na riko, Gwamna Mai Mala Buni na Yobe.
Idan Oshiomhole ko wani daga Kudu ya zama shugaban jam’iyyar, to dan Arewa ne zai kara yin takarar shugabancin kasa a zaben 2023.
Mohammed ya yi zargi cewar, gungun mutanen jiran lokacin taron jam’iyyar na kasa suke yi, sun kuma gama shirya yadda Oshiomhole zai shiga takarar shugabancin jam’iyyar.
Ya kuma yi zargin za a juya ra’ayin wadanda za a ba wa damar zaben domin Oshiomhole ya koma kujerarsa.
Mohammed ya nemi kwamitin Buni ya dauki mataki da wuri domin kauce wa matsalar da ka iya bijirowa a lokacin taron jam’iyyar.
“An yi duk kulle-kullen da za a yi na ganin Adams Oshiomhole ya shiga takarar zaben ya kuma dawo matsayinsa na Shugaban jam’iyyar APC, a babban taron jam’iyyar na kasa.
“Hakan ba matsala ba ne, sai dai matsi da tursasa shugabanin jam’iyya su dauki zaben kamar ya fi komai muhimmaci shi ne abun damuwa.
“Ya fito karara cewar Kwamaret Oshiomhole da wani sashe na kusoshin jam’iyyar APC na neman nasarar zaben ko da ta haramtacciyar hanyar ce.
“Hatta kiran da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi na a yi adalci a zaben Edo domin a ba mutane ‘yanci, ba zai hana su yin abun da suka yi niyya ba”, inji Mohammed.