✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake shiga karatun likitanci

Dole sai dalibi yana da sha’awa da juriya.

Yadda ake shiga karatun aikin likita a kasar nan ba hanya ce mai sauki ba, domin sai dalibi ya ci jarrabawar kammala makarantar sakandare iri biyu kuma da maki mai kyau.

Wadannan jarrabawa biyu su ne jarrabawar kammala sakandare ta SSCE wadda WAEC ko NECO ke shiryawa da kuma jarrabawar cancantar shiga jami’a ta UME wadda JAMB ke shiryawa.

A Jarrabawar SSCE sai dalibi ya samu akalla lamba ta Kiredit wato ajin ‘C’ ko sama da haka, ma’ana ‘B’ ko ‘A’ a bangarori biyar na Ilimin Lissafi (Mathematics) da Inglishi (English) da Ilimin Halittu (Biology) da Ilimin Sinadarai (Chemistry) da Ilimin Tsantsar Kimiyya (Physics) a zama daya ko biyu, wato ba dole sai a zaman jarrabawa daya kadai ba.

Zai iya samun lambobin Kiredit a karatu uku bana, badi ya samu a sauran biyun.

A Jarrabawar UME kuma sai dalibi ya samu maki sama da 200 a wadancan bangarori biyar, (amma akan iya cire Lissafi) a zama daya, kafin a fara tunanin sa shi a ajin masu iya karanta likitanci.

A wasu jami’o’i wannan maki zai iya kaiwa 220 ko ma 250 dangane da yawan wadanda ke neman shiga da yawan guraben karatun da jami’ar ke da shi.

Idan dalibi ya kasa samun wannan maki na 200 ko sama a Jarrabawar UME, har ila yau, akwai hanyar shiga jami’a ta ajin share-fage wato Remedial.

Daga wannan aji idan dalibi ya yi kokari sosai za a iya ba shi gurbin karatun likita.

Abin da ya sa aka tsaurara wadannan matakai na shiga aikin likita shi ne, jerin bangarorin ilimi da dalibi zai fuskanta a jami’a a tsangayar ilimin likita, su ma ba masu sauki ba ne.

Don haka sai dalibi ya samu duka maki da lambobi ne ake ganin abin ba zai ba shi wahala sosai ba.

To idan dalibi ya samu wadannan, kuma ya kasance yana da SHA’AWA da JURIYAR karanta fannin likita, to za a iya cewa ya yi mai wuyar.

Abin da ya sa aka ce sai yana da sha’awa da juriya shi ne, ko da ya ci wadannan maki da lamba, idan ya shiga karatun likita ba da sha’awa da juriya ba, zai iya barin karatun, domin karatu ne na akalla shekara biyar a jami’a, wanda kan iya kaiwa shekara 10 idan aka hada da barazanar yajin aiki da karin wasu tsarabe-tsarbe na sanin makamar aiki da kwarewa.

Ga kashe kudin littattafai da kayan karatu iri-iri. Wato ke nan sai an tsaya wa dalibi ta hanyar kudi a gida ko a makaranta (scholarship) kafin a samu dacewa.

A yanzu da abubuwa suka kara tsanani a kasar nan, an ma fi samun gurbin karatu a kasashen waje irin su kasar China da Hadaddiyar Daular Larabawa da Sudan da Ukraine da sauransu.

Wato a ’yan shekarun nan likitocinmu da akan yaye daga wasu kasashe suna ma so su fi na nan kasar.

(An wallafa wannan makala shekara biyar da suka wuce. An sake tsakuro ta domin muhimmancinta ga al’umma).