Ga dukkan alamu, shekarar 2022 ce ta karshe da dan talakan Najeriya zai tafi karatu a jami’a, ganin yadda wasu takardu masu alaka da wasu daga cikin jami’o’in ke nuna yadda ake shirin ninka kudin makaranta, ko ma dai in ce an ninka!
Ta yiwu wannan lamari yana da alaka da artabun da ke tsakanin gwamnati da malaman jami’o’i.
Ko ma dai mene ne, da gwamnati da malamai, ku tuna fa wannan dambarwa ta ku a kan ’ya’yan talakawa take karewa.
A ranar 14 ga Fabrairun 2022, Kungiyar ASUU ta shiga yajin aikin gargadi bayan ta zargi Gwamnatin Tarayya da kin cika mata alkawura.
Bayan tsawon lokaci, wannan lamari ya sa kungiyar ta yi ta zama da wakilan gwamnati.
Wani lokaci a rabu ‘barambaram’, wani lokaci kuma a rabu ana yake.
Shigar Kungiyar ASUU yajin aiki ya sa Gwamnatin Tarayya a karkashin jagorancin Shugaba Muhammadu Buhari kin biyan malaman jami’o’i kudadensu.
Dalili shi ne tabbatuwar tsarin nan na “NO WORK NO PAY,” ma’ana, babu biya in ba a yi aiki ba.
Wannan mataki ya sa Kungiyar ASUU ci gaba da zaman gida har sai da ’ya’yan kungiyar suka kwashe wata bakwai a zaune, lamarin da wasu ke ganin ya yi sanadiyar mutuwar wasu daga cikin malaman jami’o’in, wasu kuma sun shiga halin matsi.
Bayan cikar Kungiyar ASUU wata bakwai tana yajin aiki, Shugaban Majalisar Wakilai, Femi Gbajabiamila, ya yi nasarar sasanta bangarorin biyu, lamarin da ya sa shi yin fice, la’akari da cewa wadanda abin ya shafa, kamar Ministan Ilimi, Malam Adamu Adamu da Ministan Kwadago Dokta Chris Ngige sun gaza shawo kan lamarin.
Daga karshe dai ASUU ta janye yajin aikin a ranar 14 ga Oktoban 2022, bayan wata 8. Allah Ya saka wa Femi Gbajabiamila da alheri a bisa jajircewar da ya yi na sasanci tsakanin ASUU da Gwamnatin Tarayya.
Idan na dawo bangaren dalibai kuma, tsawon lokacin da suka kwashe a gida sun yi hutu ne cikin fargaba da tunanin cewa a kowane lokaci za su iya komawa makaranta.
Wannan tunani ya sa da dama daga cikin dalibai kin kama sana’a’ saboda suna gudun kada su fara ASUU ta janye yajin aikin.
Mai karatu zai iya cewa to ai ba wannan ne karon farko da ASUU ta tafi yajin aiki ba, to amma duk da haka, ko wani yajin aiki da yadda yake kasancewa.
Yajin aikin ASUU ya shafi daliban jami’o’i fiye da duk wani mai ruwa da tsaki a harkar ilimi!
Dalibin da ya kamata a ce ya kammala karatunsa na digiri a shekara hudu ba ya samun damar hakan.
Sai ka ga maimakon shekara huɗu, mutum ya kwashe shekara shida ko fiye da haka.
Bayan karin wa’adin karatu, dalibai da dama da suke da burin kammala jami’a sun hadu da ajalinsu.
Masu raunanar zuciya sun yi amfani da rauninsu wajen kwashe wa dalibai kayayyaki da suka bari a dakunan kwanansu.
Allah Sarki dalibi, bawan Allah! Idan za ka tashi hankali sai a ce kai mai ilimi ne. Allah Ya yi wa iliminka albarka. Amin.
Bayan dukkan wadannan kalubale da dalibai suka fuskanta, sai ga shi a kwanakin nan wasu daga cikin manyan jami’o’in kasar nan sun fara fitar da sababbin tsare-tsaren biyan kudi.
Wasu makarantu sun kara kaso kadan, yayin da wasu kuma suka ninka kudin da hankali ma ba zai dauka ba.
Wannan lamari ya tayar da hankalin duk wani dalibi, musamman wanda ya fito da ga gidan da ba su da karfi.
Da yawa da ga cikin dalibai sun shiga fargaba, inda wasu da dama ke tunanin ko da akwai yiwuwar su ci gaba da karatu ko kuma su hakura, su ajiye. Allah Ya ceto bayi.
Wannan dalili ya sa ni zantawa da dalibai da masu rike da ragamar gida, inda suka tabbatar min da halin da suke ciki.
“Wata rana muna zaune bayan an gama darasi, wani daga cikin malamanmu ya kunna wayarsa, sai ya nuna mana sabon jadawalin kudin makaranta da za mu rika biya nan gaba kadan,” in ji wani dalibi da ya fito daga daya daga cikin jami’oin Gwamnatin Tarayya.
“Ni nake daukar nauyin karatun kannena. Zan sa kanina daya a sabuwar makarantar koyon aikin likitanci, amma abin ya fi karfina. Yanzu mun hakura,” in ji wani da ya yi kokarin kai kaninsa jami’a.
Shi kuwa wani uba cewa ya yi “Na yi burin kai ’yata makarantar gaba da sakandare, to amma na ga abin ba mai yiwuwa ba ne.
“Yanzu na bar wa Allah komai. Ina addu’ar Allah Ya ba ni yadda zan yi na aurar da ita kawai.”
Yanzu dai shekarar 2022 ta zo karshe. Al’ummar duniya na shirye-shiryen shiga shekarar 2023. Al’ummar Najeriya, musamman dalibai na fargabar shiga sabuwar shekarar, Kasancewar ba su san da wane salo shekarar za ta zo mu su ba.
Shin akwai yiwuwar ASUU ta kara shiga yajin aiki? Shin dukkan jami’o’i za su huce haushinsu ne ta hanyar kara wa dalibai kudin makaranta?
Ko dai wani dalili zai zo da zai sa wadannan matsaloli ba za a sake fuskantarsu ba? Fatanmu shi ne Allah Ya sa daga shekarar 2022 matsalolin da suke addabar fannin ilimi sun zo karshe.
Allah Ya sa dalibai su samu damar sararawa a sabuwar shekarar da za a shiga.
Allah Ya zaunar da kowa lafiya a Najeriya da duniya baki daya. Allah Ya sa a gudanar da zabubbukan Najeriya lafiya, Ya kuma bai wa Najeriya shugabanni nagari.
Daga karshe, ina mai amfani da wannan dama wajen yin kira ga Shugaban Kasa mai shirin barin gado, da Shugaban Kasa mai rabo a zaben 2023 da ministocin da abin ya shafa masu ci da masu zuwa da dukkan ’yan majalisa da hukumomin kula da ilimi a dukkan matakai da Hukumar Kula da Jami’o’i da shugabannin jami’o’i da malamansu, da sauran masu ruwa-datsaki a harkar ilimi, a ji koken talakawa, a taimaki fannin ilimi, kana a yi duba a kan batun kara wa dalibai kudaden makaranta, domin hakan zai iya sanadin ajiye karatun da yawa daga cikin daliban.
Haruna Umar ya rubuto ne daga Jos. Za a iya samun sa ta: Imel:ibnumar613@ gmail.com. 07062579831