Abubuwan da ake bukata:-
• Burodi mai yanka-yanka
• Nama
• Attarugu
• Albasa
• Man gyada
• Kayan kanshi
• Kori
• Sinadarin dandano
Yadda ake yi:
Da farko uwargida za ta samu nama mai kyau wanda ba ya da kitse ko jijiya sai ta gyara sannan sai ta dafa shi da kayan kanshi da albasa da sinadarin dandano. Idan ya dahu sai ta daka ta kuma soya sama-sama.
Sannan sai ta samo burodi mai yanka-yanka wanda bai bushe ba sai ta dauki guda daya ta cire gefen burodin, ma’ana wurin da ya kone din nan sannan ta dora a kan katakon murji ta murza wannan burodin a hankali har ya zama kamar fulawa.
Idan ya yi fadi sai uwargida ta yi masa nadin samosa wato ‘triangle’ sannan sai ta zuba hadin naman nan mai yawa a ciki. Sai ta kwaba fulawa mai dan ruwa-ruwa sannan ta like shi.
Idan ta gama gaba daya sai ta dora kaskon suya a wuta ta zuba mai sannan ta bar shi ya yi zafi sosai sai ta zuba a ciki. An fi so sai mai ya yi zafi sosai sannan za a zuba don kada ya sha mai kasancewar shi samosan na burodi ne ba kamar na fulawa ba. Shi ke nan idan ya soyu ya yi launin ruwan kasa sai a tsame.