✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake ‘pan cake’ din ayaba

Akwai hanyoyi da dama na sarrafa ‘pan cake.’ Kowace mace na da irin nata yanayin sarrafa girki, shi ya sa a kullum nake kara tunatar…

Akwai hanyoyi da dama na sarrafa ‘pan cake.’ Kowace mace na da irin nata yanayin sarrafa girki, shi ya sa a kullum nake kara tunatar da mu a kan cewa yana da kyau mace ta kasance mai sarrafa sabon abu a kullum. Koda tuwo ne, yana da kyau a kasance ana canja na’ukan miya domin kara wa abinci armashi da kuma kin fita ran masu ci. A yau na kawo muku yadda ake sarrafa ‘pan cake’ din ayaba. A ci dadi lafiya.

Abubuwan da za a bukata

• Ayaba

• kwai biyu

• Madara

•Bata

• Sukari

• Fulawa

Hadi

A samu na’urar markada kayan miya (blender), sannan a yayyanka ayabar a ciki. Bayan haka, sai a fasa kwai biyu a ciki, sannan a zuba bata (butter) kamar cokali uku zuwa hudu. Daga nan sai a zuba madarar ruwa ko a kwaba da madarar gari da ruwa sannan a zuba. A zuba sukari da garin fulawa kadan, sai a rufe na’urar a markada su, har sai sun yi laushi sannan a  sha.

A dora tukunya mara kama girki a wuta (non-stick) bayan ta yi zafi, sai a rika debo kullun ayaba ana zuba shi ta irin yanayin da ake so. Idan ya dan nuna, sai a juya dayan gefen domin shi ma ya gasu. Sannan a kwashe.

Za a iya cin wannan hadin da zuma ko da miya. Wannan abincin an fi yin sa ne a matsayin abincin karyawa.