Barkanmu da sake saduwa daku Uwargida a cikin wannan filin namu na girke-girke. A yau na kawo muku yadda ake hadin salad din kaza. Yana da kyau Uwargida ko Amarya su kasance da gwada nau’ukan girke-girke domin kwarewa a wadannan fannin girki yadda zasu hana maigida zuwa wani waje cin abinci. Domin kara kwarewa da nau’ukan girki, sai a kasance tare da shafinmu na girke-girke a cikin jaridar Aminiya a kowa ne mako.
Abubuwan da za’a bukata
• Kaza
• Dakakken masoro
• Nikakken citta
• Garin tafarnuwa
• Kori
• Man zaitun
• Borkono (ga mai bukata)
• Kabeji
• Timatir
• Gurji
• Albasa
Hadi
Da farko dai za’a wanke kaza a kuma cire karninsa kamar yadda na yi bayani a baya. Bayan haka sai a yayyanka shi sannan a zuba a roba. Sannan a zuba nikakken masoro da garin citta da garin tafarnuwa da kori da dakakken borkono ga mai bukata sannan a zuba cokula biyu na man zaitun sannan a cakudasu sannan a zuba a leda a sanyasu a firiji na tsawon a wanni biyu zuwa uku. Bayan haka sannan a shiga gasasu akan rushin wuta ko kuma na’urar yin gashi har sai kaza ta gasu. Sannan a kwashe a ajiye a gefe.
Sannan a yayyanko kabeji kanana da albasa da kuma gurji sannan a zuba su a ciki a cakudasu sai a sake yaryada soyayyen man zaitun din kadan akai da magi.
Za’a iya cin wannan hadin da jus din lemun zaki mai sanyi. A ci dadi lafiya!