✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake hada lemon Na’a-na’a

Yau a filinmu na Girke-girken Azumi za mu kawo muku yadda ake hada Lemon Na’a-na’a

Assalamu Alaikum uwargida, barka da rana.

Yau a filinmu na Girke-girken Azumi za mu kawo muku yadda ake hada Lemon Na’a-na’a.

Ga kayan hadin da uwargida ke bukata:
Ganyen Na’a-na’a
Lemon tsami
Sukari
Fulebo
Yadda ake yi:
  • Uwargida za ki sami ganyen Na’a-na’a sai ki wanke tas sannan sai ki markada shi.
  • Sannan sai ki sami lemon tsami ki matse.
  • Sai ki hada ki tace.
  • Sannan  sai ki dafa sukarinki.
  • Sai ki sami babban kwano ki hada lemon ki juye dukkanin ruwan Na’a-na’a da na lemon tsami da kika tace a ciki sannan ki dauko dafaffen sukari da fulebo ki zuba.
  • Sai ki sa shi a naurar sanyaya kayayyaki (fridge), ko ki sami kankara ki zuba a ciki.
A sha ruwa lafiya.