✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda ake girka Kalwale

Yadda ake girka Kalwale

Assalamu Alaikum Uwargida, yaya azumi?

Yau muna dauke da bayani kan yadda ake girka Kalwale.

Ga kayan da ake bukata na hadi:

Wake

Agada

Man gyada

Attarugu

Albasa

Sinadarin dandano

Gishiri

Tafarnuwa

Masoro

Danyar Citta

Koren tattasai (Sweet pepper)

Yadda ake girkin

Da farko uwargida za ki dafa wake ki ajiye shi a gefe sai ki yayyanka agada sai ki soya ta a ciki mai ki ajiye a gefe.

Sannan sai ki dauki kwanon suya ki zuba mai kadan a ciki, ki zuba yankakkiyar albasa mai dan yawa a ciki ki soya.

Daga nan sai ki zuba dakakken masoro da tafarnuwa a kai ki ci gaba da soyawa.

Idan ya fara yin ja sai ki kawo jajjagen attarugu ki zuba a kai ki zuba dakakkiyar danyar citta kadan a kai ki ci gaba da juyawa.

Daga nan sai ki dauko waken nan da kika dafa ki juye a kan wannan soyayyen kayan miyar ki zuba gishiri da sinadarin dandano ki ci gaba da soyawa.

Idan ya yi kamar minti 10 sai ki dauko soyayyiyar agada ki zuba akai ki juya yadda za su hadu.

Sannan sai ki kawo yankakken koren tattasai ki zuba a kai. Ki kara juyawa. Shi ke nan Kalwale ya hadu sai ci.

A ci dadi lafiya.