Assalamu alaikum Uwargida tare da fatan ana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku wani nau’in girki da idan aka yi tabbas za a samu canjin dandano a gida. Shin da mene ne ake cin farar shinkafa a gidanku? Inji dai ba da miyar dage-dage ba ce kawai? In ko haka ne har yanzu da sauranku a girki, sai a matso kusa a dauki sabon darasi. Miyar ‘Chicken curry’ dai miya ce ta kasar Indiya wadda ake hadawa da shinkafa domin kara dadi da gardi da kuma dandano.
Abubuwan da za a bukata
• Kaza
• Kori
• Bata
• Nono
• Tafarnuwa
• Citta
• Albasa
• Karas
• ‘Peas’
• Koren wake
• Magi
Hadi
Idan Uwargida ta wanke naman kaza tsaf kamar yadda muka yi bayani a baya yadda ake cire karni, sai ta yayyanka kanana sosai yadda za ta raba fatar da kashi sannan ta ajiye a gefe.
Sai ta dora tukunyarta mara kama girki (non-stick) sannan ta zuba bata ko man zaitun isasshe sannan ta zuba naman kazar da ta riga ta yayyanka a ciki ta yi ta gaurayawa har sai hadin ya fara nuna sannan ta dauko kori mai kyau mai kuma kanshi ta zuba kamar cokali biyu sai ta ci gaba da gaurayawa.
Sannan ta dauko albasa kanana ta watsa tare da jajjagen attarugu da tafarnuwa da citta ta zuba sannan ta debo nono ko madara mara sukari ta zuba a ciki ta ci gaba da gaurayawa sannan ta zuba magi ta dan rufe na tsawon minti biyu sannan ta sake budewa.
A wannan karon za ta zuba yankakken karas da koren wake sannan ta gauraya ta rufe. Bayan minti daya sai ta zuba ‘Peas’ ta ci gaba da gaurayawa sannan ta sauke. Sai a zuba a kan farar shinkafa a ci.